Pr ads

Photography

 

Download Music : ROMEO44 X QBENZ X USAINA ONGAS X CHIZAMANI X DBEM X MEDONE_2021
 

ROMEO44 X QBENZ X USAINA ONGAS X CHIZAMANI X DBEM X MEDONE_2021 CYPHER The famous Arewa upcoming rappers from zaria back again with their international and hottest song/cypher that have never hear before title 2021 cypher 
Street to download it and share it to your friends Download

DJ AB NASON DAUKAR SABABBN YARA.


Dj Ab Nason Daukar Sababbin Yara.


Tauraron wakan hip-hop mai suna Dj Ab Dan asalin Jahar Kaduna yasanya wata gasa wacce taja hankali sosai musamman ga mawaka na hip-hop din masu tasowa.


Ya shaidawa Mutane cewa ya Sanya gasa ta Waka ga Dukkanin Wanda yayi tayi kyau sosai tayi Dadi Kuma ta bada ma'ana zai daukeshi Kuma ya taimaka Masa sosai a harkar Waka. 


Karanta Wannan >> Mawakan Hausa Hip-Hip Uku Da Sukayi Fice A Arewa.


Baya bukatan kaje studio ka buga wakan ka tura Masa kafin ka Shiga gasar shidau kawai Yana Bukatar ne kayita a rubuce.


Ya fitar sa sanarwar ne a shafinsa na (Facebook page ) Idan baka dashi sai jayi searchin dinsa zaka iya dubawa a Wannan hoton da yake kasa donin kaganewa idonka kokuma kaje ka duba a page din mai suna (DjAbba Abdullahi).
Yanasone Kasanya ( Kome zai faru yafaru ) acikin wakar saikaje Shafin nasa na Facebook kaduba Wannan posting din nasa sai kayi comments.


Karanta Wannan >> Tarihin Ali Nuhu.


Idan yagani Kuma yayi yanda yakeso zaiyi maka magana privately saiya fada maka duk yanda ya shirya abin.

HANYOYIN KARA KIBA.Barka dazuwa wannan shafin namu wanda a yau zamuyi bayani akan abubuwanda suke saka mutum kiba akwaisu dayawa Amma zamu kawo muku misali dakuma Wanda yadace ayi amfani dashi.


Akwai abubuwa da dama da suke sanya mutum kiba Wanda Kuma wasu daga ciki suna cutarwa dukda zamu kawosu saboda kusansu Amma kuma zaifi kyau kuyi amfani da Wanda muka baku a shawara akai tunda angwada anga Yana aiki yanda yakama.


1. Yawan Shan zaki : Yana sanya mutum kiba kiba dukda munsani cewa zaki Yana iya haifar da wasu cututtuka a jikin Dan adam Amma bazamu dauki wannan a matsayin abinda zamuyi amfani dashi wurin kara kiba ba.


Karanta wannan >> Yadda ake sarrafa fulawa.


2. Yawan cin maiko : Shima yawan cin maiko Yana  sanya mutum kiba Kuma munsan maiko abune da muke amfani dashi yau da kullum. 


3. Rashin  motsa jiki : kowa yasan komai kibarka indai kana motsa jiki yanda ya kamata to sai kibarka ta ragu musamman idan kana gudu, kwallo, da sauran wasu aikace-aikace da gida da zasu zamto ana motsa jiki ne.


4. Cin  naman saniya : Naman saniya Yana matukar taimakawa wajen kara kiba dukda shima akwai  shekarun da idan kakai zai zamo maka illa kamar yadda masana suka fada Yana iya zamawa mutum a cinya kamata yayi kamar daga shekara 50 ko kasa da hakama ka kaucewa cin naman saniya saika kima kifi ko naman zabo, dawisu, kajin hausa da Naman tantabara zaifi kyau ga lafiyarka.


Karanta wannan >> Yadda ake gurasa.


5. Yawan cin protein : Cin protein kamar kwai a wasu lokutan muna daukan cin kwai a matsayin jindadi ne muci dayawa aa ka'ida shine kaci daya a Rana shine zaiyima amfani Kuma zai taimaka maka wajen kara kiba.


HANYAR DAYA DACE KUBI DOMIN KARA KIBA.


Wannan hanyar da zamuyi bayani yanzu itace da dace mutum yabi wurin kara kiba domin ba kwaya bace ta bature kokuma wani sassaken itace aa kunu ne akeyi asha batare da wani damuwa ba.


ABUBUWAN DA ZA'A SAMU.


1. Waken soya cokali biyu.

2.Ridi cokali biyu.

3. Dabino guda biyar.

4. Hulba cokali daya.

5. Gyada dai dai misali. 

6. Madarar gari cokali biyar.


Karanta wannan >> Zafafan kalaman soyayya.

 

yadda zaku hada ku soya waken soyan harsai yafara kamshi sai sauke a nika kokuma daka ya zamto gari shima ridin haka zaku masa ku soya shi ku mayar dashi gari  shima wannan dabinon ku daka yakoma gari ku hada da hulbar da madarar itakuma gyadar sai a hada kunun gyada da ita saiku dinga diban wancan abubuwan da kuka hada kunayin kunun harna tsawon sati biyu zakuyi mamaki.

YADDA AKE SARRAFA FULAWA.


Yadda ake sarrafa fulawa acikin sauki kamar yadda muka sani fulawa ana iya sarrafa ta abubuwa da yawan gaske Wanda yanzu yakasance kusan  zamu iya cewa kaso saba'in da cikin abincin da mukeci duk fulawa ne musamman a arewacin kasarmu ta nigeria.


Sabida haka mukaga yadace mu kawo muku hanyoyi kala-kala na yadda zaku sarrafa taku fulawar wata kila kunayin wani Abu daban Kuma ya isheku Kuna bukatar ku sauya want kunga wannan zai matukar taimaka muku.


Abunda yake yanzu ya kamata muyi zamu lissafo muku abubuwan da akeyi da fulawa cikin sauki dukda dai wasu anayinsu da oven abin gasawa wasu Kuma akan soyasu a Mai Amma sai zaku duba kuga Wanda zaku iyayi sannan bayn mun lissafu zamuyi cikakken bayani akan guda daya Wanda daga baya zamuci gaba.


ABUBUWAN DA AKEYI DA FULAWA.


1. Concot.
2. Cin-cin.
3. Gurasa.
4. Donot.
5. Taliya.
6. Dubulan.
7. Bredi.
8. Cake.
9. Meat/fish pie.
10. Fanke.
11. Biskit.
12. Dan-wake.
13. Wainar fulawa.
14. Alkubus.
15. Funkasau.


Karanta wannan >> Hanyoyin samun kudi.


Ga kadan nan na lissafo daga cikin abubuwan da akeyi da fulawa dukda nasan ko rabi ban fado bah amma nasan wadannan ma zaku karu dasu sosai idan Allah ya yarda Kuma zamu dauki daya aciki muyishi ta yadda kowa zai fahimta.


Zamu dauki na farko wato (concot) Wanda gaskiya kamar zai Zama bako sabo daga cikin abubuwan Dana lissafo shiyasa na dauko Shi domin nayi Mana bayaninsa Kuma bawai you agida kawai ba zaku iyayi domin sana'a ce sosai Kuma yanada matukar riba Mai yawa.


YADDA AKE CONCOT.


Abubuwan da zaka nema kafin ka kwaba Shi saika tabbatar suna gefenka sabida gudun kar afara azo arasa wani abun kunga shiri ba baci kenan sedai ayi wani abun ko afasayi gaba daya.


1. Fulawa.
2. Sugar.
4. Yeast.
5. Baking powder.
6. Gishiri.
7. Manja.
8. Man gyada.


Wadannan sune jerin abubuwan da zamuyi amfani dasu wajen Yin wannan concot din saiku natsu ku karanta dakyau sabida gudun kuskure kar azo ayi baiyiba ko baiyi dadi ba kunga Rai bazaiso hanaka ba Don haka zamu fara.


Karanta wannan >> Hausa Novels littafin kanwar mister.


Asamu baho Wanda za'a kwaba aciki sai a zuba fulawan asaka sugar da baking powder sai asaka gishi kadan da manja sabida yayi ja yafi bayar da kala kowa yagani zaiyi sha'awarsa.


Sai asamu ruwan zafi Amma fa ba zafi sosaiba dumi dai kawai kada yazama yayi sanyi dai sai akwaba dashi sannan kuma kwabin yayi tauri bawai ruwaba sai adauka akai gidan biredi aci su nikashi a injin Nika biredi saiku biyasu baya wuce naira hamsin zuwa dari.


Dagana ana kawo Shi zakuga yayi laushi sosai saiku samu faranti na silver ku yanko kadan kusa saikusa kwalabar coke ko tawani Abu kuyi Fadi dashi ku yankashi kamar yanda kuka gani a wannan hoton da yake kasa.


Shikenan saiku yankashi duka kusa a keda Mai Fadi idan baiyi tashi ba saiku samu wani ledan Shima me Fadi ku rufeshi zakuga ya tashi ya kumbura shikenan saiku Dora Mai a wuta yayi zafi saikusa albasa ku soyashi yayi kamshi sai ku dinga dauka Kuna siyawa a cikin man gyadan.


Idan nagida ne Wanda zakuci duk yanayin girman da kukayi Babu damuwa Amma idan na sayarwa ne zaku tsaya dakyau ku daidaita girmansa sabida yanayin abubuwan anayin sana'a Don riba ne idan yayi girma dayawa kunga baza'a fitaba.


Karanta wannan >> Yadda ake gurasa me dadi.


Bayani Wanda kuka zuba a cikin man gyada yasoyu zaku ganshi yayi jyau yayi Shar tayadda ko fita akayi dashi za'a sayar dashi da sauri Shima ga yanayin yadda yakeyi a wannan hoton Shima da yake kasa.


Nan muka kawon karshen wannan Shirin na filin girke-girke saikuma idan munhadu a gaba
Mungode.HANYOYIN SAMUN KUDI || ZAZZAULOADED.COM.NGBarkanku da zuwa wannan shafin namu Wanda muka saba kawo muku abubuwan daban-daban ayau hanyar da mukazo muku da ita hanyoyi ne da zaka samu kudi dasu idan kabin abin yadda yake tareda bayarda shawar-wari.


Idan mukace hanyoyin samun kudi bawai muna magana akan Abu daya kacan bane aa muna magana ne akan abubuwa dayawa ma'ana haryar ba guda daya bace kacal.


Zamu fara da bangaren sana'a tareda yimuku bayani akai dakuma yadda zakayi domin ganin mun hadu mun kawar da rashin aikinyi kokuma domin kawar da talauci a wannan lokacin musamman yanda abubuwan suka chanja.


Akwai sana'oi daban-daban Wanda mace zatayi namiji Shima zaiyi dukda cewa wasu lokutan muna raina sana'ar ne muna ganin munfi karfinta kuma Sam bahaka bane dukkanin hanyar da akace za'a samu kudi to baikamata ace anyi Wasa da ita ba.


Karanta wannan >> Yadda ake gurasa.


Musamman ga yara samari kabar gani kana makaranta idan yazamto bakada sana'a Babu Mai tallafa maka tayaya karatun zai yiwu, haka Suma yan'mata akwai sana'oin da suna zaune a gida kokuma a kofar gida zasuyi Kuma su Sami abinda sukeso ko Babu yawa.


DAGA CIKIN SANA'OIN DA MATA ZASU IYAYI.


1. Alawar madara.
2. Gurasa.
3. Cin-cin.
4. Zobo.
5. Kunun aya.
6. Donot.
7. Awara.
8. Fanke.
9. Koko ko kunu.
10. Gyada.


Wadannan dana lissafa guda goma duka kananun sana'oi ne Wanda mace zata iya dogara dasu matukar zata tsaya ta gyara bama iya mace ba har maza akwai Wanda zasu iyayi kamar cin-cin, donot, dakuma gurasa.


Sannan akwai saye da sayarwa kamar kasiyo Abu naira goma kasayar naira goma Sha biyar akwai kayan su Maggi dasu omo duk wannan abun hanyoyine da mutum zai samu kudi Amma Wai kaga mutum yarasa sana'a sedai bashi da niyyar yin sana'a.


SANA'OIN DA MAZA ZASU IYAYI.


To shudai namiji ba kamar mace bane zai iya fita ko'ina domin yaga yasamu abinda zai rufa ma kansa asiri ba lallai sai sana'ar wuri daya ba zaka iya talla ka dinga zagawa ba lallai sai area dinku ba sai katafi wani wurin daban idan bazaka iyayi a unguwarku ba daika nemi sana'a kamar ;


1. Wankin mota.
2. Wankin Kaya.
3. Gyaran takalmi.
5. Kodago.
6. Aikin gini.
7. Sana'ar shayi.
8. Yankan farce.
9. Guga.
10. Aikin fawa.


Wannan Dana lissafo kusan kowa zai iyayi indai namiji ne Kuma yawanci basaida jari ba mutum zaifara Wanda yake bukatar jari shine kamar shayi haka wannan Saida jari Amma akwai dabarorin sana'a da zamu kawo duk zaku fahinta komai cikin sauki.


Karanta wannan >> Zafafan kalaman soyayya.


Amma kafin naje ga wannan zanyi wani bayani yakamata yara suna kanana a kaisu waje koyar aiki ta yadda yaro zai taso da sana'arsa a hannu ba tareda ya wahala ba akwai wajen sana'oi da dama kamar koyan dinki, walda, kanikanci gyaran mashin da mota.


DABARORIN SANA'A.


Idan ya kasance bakada kudi Kuma kanason yin sana'a to meyakata kayi ? Kanemo duk abinda kake buka misaki zakayi alawar madara daga cikin abubuwan da ake hadawa akwai madara, sugar sai itacen da zaka dafa sugar din da flavor.


Saikaje wurin me madara kuyi magana yabaka madara idan kayi kasayar zaka bashi kudin sai ka dauki wata sabuwa haka me sugar dama dai duk abunda kake da bukata kafin fara wannan sana'a idan yabaka kaga bakada damuwa saika fara sana'arka.


Kanayi tun ahaka ribar da kake samu idan katara shikenan sai jarin yazama naka kaga kayj dabara tun baka da kudi har kasamu naka sai kaci gaba da juyawa kudin harma idan kanason gwada wata sana'ar saikayi.


Karanta wannan >> Bayani akan zaman aure.


Akwai Kuma sana'ar kamfani kamar inda sukeyin pure water ko bread kodai wani abun Suma zaka iya zuwa kasamu manager na kamfanin kuyi magana akan idan kadauki Kaya kasayar zaka dawo da kudin abaka wani kayan.

SABON TSARIN MTN NIGHT BROWSING.Sabon tsarin mtn night browsing tsarine a baya da ake siyan data me sauki ake amfani da ita tsawon wasu awanni kamar yanda muka sani bawai data bane da takeyin amfani har wasu kwananki kokuma watanni.


Zamuyi bayani yadda abun yake domin wadanda basusaniba Suma zasu iya amfani da wannan damar suma suci gajiyar wannan datar domin tanada sauki sosai Kuma tanada yawa.


Wannan datar tabbas dukda Bata da tsawon awanni amma Kuma zatayi maka dukkan wani irin Abu da zakayi a yanar gizo Kuma wadanda zasuci fin moriyar wannan to masu downloading na video,waka,app da sauran abubuwa.


Kuma bawai anwareta bane ance iya Abu daya zakayi ba kunsan akwai datar da takeyin Facebook zallah akwai wacce take whatsapp itama sannan akwai datar Instagram to it' wannan ba'a ware ance ga ta Abu daya ba zakayi dukkan abinda akeyi a yanar gizo (internet).

Karanta wannan >> Farashin datar mtn a 2020.

Datar tana daukar tsawon awa  bakwai (7hrs) zuwa awa takwas (8hrs) ana amfani da ita Saida Kuma a wannan kwanakin ne kamfanin mtn ya chanja tsarin ba kamar yadda muka sani a baya ba Don haka yanzu zanyi bayanin bambamcin da aka samu tsakani.


Duk wani Wanda yake night browsing yasan cewa ana farawa ne misalin karfe shabiyu na zuwa karfe biyar na asuba inda yanzu Kuma tsarin ya chanja zaka iya siya misalin shadayan dare Kuma kayi amfani da ita a maimakon shabiyun.


Amma Kuma zaka iya siyan datar kafin lokacin amfaninta ya fara kamar karfe gima misali kasiya saikuma karfe shadaya kafara amfani da datarka babu wani matsala a maimakon sai lokacin yayi da zaka fara ka tsaya ka siya.


Abaya zaka iya siyan 500mb ne kacan inda yanzu Kuma suka kara zaka iya siyan datar takai 1gb kunga ansamu kari kenan akan yadda ake siya a baya zaka iya siyan 250mb har sau biyu kokuma 500mb sau daya yanzu kuma 500mb sau biyu kokuma 250mb sau hudu.


Ga wadanda sababbi ne a harkar wannan datar sukeso Susan yadda akeyi to yanzu zanyi bayaninta yadda zakayi daga farko har zuwa karshe Amma dai ka tabbatar layinka mtn pulse ne domin shine layi daya tilo da yakeyi.

Karanta wannan >>Bayani akan zaman aure.

Idan Kuma ba a tsarin MTN pulse kake ba to zaka iya mayar da layinka yakoma MTN pulse din cikin minti biyar ba sai an Dade ba Amma dai kawai ka tabbatar akwai katin naira dari a layin domin idan bahaka ba bazaiyi ba.


YADDA AKE KOMAWA MTN PULSE.


Ka saka katin naira dari a layin idan Kuma akwai aciki shikenan sai ka danna *496*1# shikenan sai kayi migrating zasuyi maka massage kana fita kaduba zakaga tsarin naka ya chanja zuwa MTN pulse din da kake bukata.


FARASHIN DATAR.


Duk 250mb ana sayarwa kan naira ashirin da biyar (N25) kokuma kasiya 500mb naira hamsin (N50) kunga kuwa ai wannan datar tayi sauki sosai za'a ci moriyarta kwarai da gaske domin bana tunanin akwai wacce takai wannan sauki.


YADDA AKE SAYAN DATAR MTN NIGHT BROWSING.


Bayan kasa kudi a layinka kukuma daman akwai kudi na iya adadin datar da kakeso Amma yazama kudin sunkai saika dannan *406*3# shikenan saika zaba ta nawa kakeso kasiya idan takare zaka iya kara siya domin kaci gaba da aiki da ita.

LITTAFIN KANWAR MINISTER KASHI NA DAYA (1).
KASHI NA DAYA (1).


University of Maiduguri (Unimaid) misalin karfe tara da rabi na safe 9:00Am yanayin garin kamar za'ayi ruwa amma ba damuna ake ciki ba kenan ba ruwan za'ayi ba saidai sama cike take taf da hadari

Makarantar cike take da ɗalibai fam kowa na jiran a shiga lecture, Wata mota ce kirar land rover pink colour tashigo cikin makarantar.

Da kaga motar kasan taji kuɗi wajen siyanta
Saida ta tsaya a motar ta amsa kira kafin ta fito da kafarta guda ɗaya a waje.

Ta ɗauki lokaci kafin ta fito gabaɗayanta wata shegiyar doguwar riga ce a jikinta ta atamfa amma kuma tamkar ba atamfa ba saboda wata irin Ado da akayi mata daga sama light pink ne kayan dakuma fari-fari a jikinta sai kuma wata kyalle da aka ɗaura a kwankwasonta kamar zata gaɗa.

Karanta wannan >> Yadda ake gurasa me dadi.

Saikuma glass ɗin da ta sanya manya-manya brown color kanta kuma yaji wata zazzafan kitso idan kaga kitson zaka zata gashin doki ne amma inaa tsantsar gashine da ita saikuma ɗankwalinda ta ɗaura na kayan me bala'in kyau

Sai kuma wata karamar jaka hannunta pink color cover wayarta ma pink color ce, Yarinyar fara ce doguwa siririya ga hanci ga kuma idanu masu kyau.

Takalman kafarta ma cover shoe ce pink color saman tana wani kyalli Waigowa inda ta hango ƴan department nasu tsaye da takaddu sai kallonta sukeyi.

Bayannan bata sake kallon kowa ba tawuce inda tasaba tsayawa ita kaɗai tafara danna wayarta maimakon tayi karatun littafi tunda yau text suke dashi

Tunda tafito daga mota kowa yamayarda kallonshi kanta amma ina kota kansu bata bi ba saboda idan tashigo makarantar bata kallon kan kowa da gashi.

Karanta wannan >> Yadda ake samosa.

Karfe tara da rabi tayi kowa da kowa yakoma department nashi saboda gaba ɗaya makarantar general ake dashi wato English Language.

Saida kowa yagama shiga har anfara yin test ɗin kafin Meera ta ɗago kai daga danna wayar da take
Taku tafara ɗas-ɗas kamar bazata taka kasa ba kuma kamar zatayi kuka saboda wai ta gaji.

Dai-dai bakin ajin ta tsaya taɗan duba lokaci ba laifi yau takara mintuna shida ne, Shiga cikin ajin tayi taje tasamu waje a baya wadda yake nata ne ita kaɗai babu wanda ya isa ya zauna mata a sit koda batazo ba.

Karanta wannan >> Abubuwan da suke kawo mutuwar aure.

Wani lecturer ne ya fusata saboda wannan rashin kunya da tayi musu Yunkura yayi zaije yafitarda ita sai wani abokin aikinshi ya rikeshi ta baya yace
"Bakada hankali ne Abdul bakasan wacece ita bako?"

"Nasir ko wacece ita sai ta fitamin daga aji yau yarinya tunda nazo na hangota daga waje amma sai yanzu zata shigomin aji" yafaɗa yana menuna alamar ɓacin rai.

"Abdul nayi mamaki ace duk zamanka a wannan makarantar bakasan wacece Meera ba" inji Naseer

"Abdul yau fa ko ubanta ne me makarantar saita barmin aji idan yaso daga baya sai a koreni donni bazan ɗauki raini ba" inji Abdul kana ya wufce rigarshi yabar wajen

Dai-dai inda take ya tsaya kem yakasa taɓuka komai saboda mamakin yadda ya ganta

Cikin dauriya yace "kee bakida hankali ne ana test zaki shigo latti kuma kinzo da wuri bayan haka kinshigo kiyi test mana amma chatting naki kikeyi a ruwanki" Abdul ne yake ta maganarshi shi kaɗai

Ko juyowa ta ganshi batayi ba saboda bataji ma meyake faɗa ba, Cikin ɓacin rai ya wafce wayar dake hannunta jikake cas alamar wayar ta suɓuce a hannunshi

Bada sonshi ba shima wayar tafashe amma saiya dake kamar da gan-gan yayi Mikewa tayi cikin sauri tana so taga wanda yayi mata wannan aikin domin bata taɓa tsumayin haka ba.

Cikin masifa tace "kai har waye dazaka fasamin waya? Waye ubanka? Waye uwarka? Suwaye danginka a garinna? kasan wacece ni? kasan daga wani gida nafito?" tareda wanke shi da mari takuma cewa "amsamin!!"

Cikin bakin ciki Abdul yaɗago kanshi wai yau macece ta mare shi abun da mamaki sai kuma yayi wata murmushi alamar bai damu ba ya ɗago kai

Yace "kema waye ubanki? Wacece uwarki? Kinsan ni waye?"

Tace "To bara kaji ni kanwar minista ce kuma zan iya sawa a ɗaure dukkanin ƴan gidanku dama danginku gaba ɗaya wato tsabar bakinciki wayata zaka fasa saboda bakada irinta ko to yau dani da kai acikin school ɗinnan saika biyata kokuma nasa a ɗaure danginka baki ɗaya a yau"

Daga yatsarshi yayi zaiyi magana Abokinshi Nasir ya janye shi daga wajen Itako Meera bata hakura ba ta ɗauki fasasshiyar wayarta tabi bayansu cikin sauri tace dolene yabiyata wayanta

Ya mika hannu ya karɓi wayara kamar dagaske yaji tsoro kawai sai yasake doka wayar da kasa Yace "ba dangina ba idan kuɗin ministarda kike ikirari zai iya kulleni ni kaɗai to ki gwada a yau kiga abin mamaki".

Saura kaɗan ta zabga ihu ganin yadda yakarasa fasa mata waya tayi kaca-kaca baka gane komai a cikinta sai dai kawai tayi shirune saboda kada ta zubda class nata acikin school don ga kowa ya taru yana kallonsu

Hannu ta ɗaga tasake kai mishi mari a karo na biyu Abinda baiyi zato ba kenan yakuma ji yadda yarinya karama ke zubar mishi class acikin makaranta.

Shima yaɗaga hannu zai zabga matamari kenan sai Nasir yarike hannunshi yace "Haba Abdul ita macece fa"

Karanta wannan >> Zafafan kalaman soyayya.

Kokarim kwatar hannunshi yake amma ina yakasa saboda Nasir ya danne sosai sai kawai yafashe da kukan bakin ciki

Ita kuma Meera ta ɗaga wayarta daga kasa tace "matsiyaci kawai daka mareni yau da wannan kazamar hannun naka sai nasa an yanketa wallahi banza jinin matsiyata sannan kasani duk sanda kaganni ka canja hanya domin bazaka fasamin waya a bulus ba ɗan iska shege"

Ɗalibanda suke tsaye ne suka kwashe da dariyar asara Kasa ɗagowa Abdul yayi saboda tsananin kunya daya shiga saida ɗaloban suka fara raguwa sannan Nasir yarike hannunshi suka bar wajen amma har yanzu bai ɗaga kai ba saboda a mugun kunyace yake.

Suna zuwa office Nasir yace "kaga abinda nake faɗa maka nace maka kada kayiwa wannan fitsararriyar yarinyar magana amma sam kaki jina yanzu ga abin kunyarda ta jawo mana"

Sai a lokacin Abdul ya ɗago kai yace "Nasir idan har ni namiji ne sai na rama abinda wannan yarinyar tayimin bazan taɓa kyaleta ba"

Nasir yace "kajika ai da shegen wauta yanzu wanda ta ɗan maka bai isheka ba kenan ko?to wallahi gwamma ka daina tun wuri"

Abdul yace "Nasir wallahi na ɗauki Alkawari idan dai ina raye wannan yarinyar tana raye saina rama wannan abinda tayi min kota halin kaka"

Haka dai sukayita yi Nasir yahakura yabarshi akan bakarshi na sai ya rama

Ita kuwa Meera tana barin wajen ba inda ta nufa sai wajen motarta shiga tayi ta kifa kanta kan sitiyarin motar tafara kuka sosai domin kaf cikin wayoyinta babu wanda takeso kamar wannan gashi da tsada yaune tayi amfani dashi na biyu kuma yayanta ne yasiya mata motar tayiwa key tabar cikin makarantar tareda aniyar ɗaukar fansa domin bazata taɓa bari haka a banza yafasa mata waya ba saita rama.

Wannan shine kashi na farko saikuma kujiramu domin kawo muku na biyu ku kasance da wannan shafin namu a kida yaushe muna godiya.
ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA.
Barkanku da shigowa wanna shafin namu musamman wannan Shirin da zamu baku samfurin kalaman soyayya a wannan zauren namu na zauren masoya, saiku tsaya dakyau wannan wanna dai na maza ne Amma kuma mata zasu iya amfani dashi saisu juyashi misali inda akace kinzamo saiki rubuta kazamo fatan zaku ji dadin wannan kalamai.


1. Inama ace nazamo a tare dake a dukkanin bugun numfashi na kaunarki kullum tana Kara girma a cikin zuciya ta dake nake kwana masoyiyata a zuciyana haka kuma dake nake tashi bayyanar murmushinki a fuskarki Yana karamin shauki a kids yaushe.

2. Masoyiyata kisani Allah ya azurta rayuwarki da abinda mata dayawa suke da burin samu Amma Basu samuba kisani ke ta daban ce a cikin zuciya ta Kuma haka nima ina fatan na zamo na musamman a cikin zuciyarki abar kaunata.

3. Rabin rayuwata kisani hakika mata irinku kadan ne domin da za'a kawo mini littafi da abin rubutu na rubuta irin baiwar da Allah yayi Miki da nayi littafai dayawa cike da tarin kalmomi ke ta musamman ce a wurina.

4. Idan kika daga kanki da daddare zakiga sararin samaniya cike da taurari shikuma teku cike da ruwa doron kasa Kuma cike da ciyayi Amma Ni cikin zuciyata cike take da soyayyarki babu kuma sauran wurin da za'asa want Abu.


Karanta wannan >> Bayani akan zaman aure


5. Kafin na kwanta bacci ina kwantawa da tunaninki haka Kuma idan ina barci nakanyi mafarkinki dazarar na farka saina kalli hotonki sannan nake jin Dadi na dawo cikin hankalina.

6. Soyayyarmu ni dake ba Mai karewa bace domin ko Bayan babu Raina kema babu ranki to hakika ruhina da naki suna atare har lokacin da zamu hade a aljanna a matsayin mata da miji.

7. Ki tausaya wa zuciyar datayi nisan a kaunarki harta kusa nakasa kada zugar mahassada tasa ki juya mata baya domin hakan shin zai haifar min da raunin da bazai taba warkewa ba azuciyata.

8. Tsananin kaunarki ya dankare a cikin zuciyata kamar yadda kwakwalwar dan'adam take a dankare a kansa ki tallafa ma zuciya ta kada ki sanya tayi hawaye da zata iya fitowa Dana fito Miki da ita domin ki Kara gasgata zancena.

9. Amincin Allah ya Kara tabbata a gareki yake wacce tafi tauraro da dukwani haske a idanuwana ina fatan kina lafiya kamar yanda nake a koda yaushe ina yawan tunaninki domin babu wani Abu da zaisa na Manta dake ba.

10. Hakika daga jiya zuwa yau wani bakon bakinciki ya bakunci zuciyata dalili kuwa shine rashin Jin munyarki da banyiba duk inda kike Ina fatan dai kina lafiya.

11. Me kaunata kece farincikin Raina Kuma kece kofar zuciyata dukkanin Wanda zai shiga ke zai taarar idan kikaga want to tabbas ke kika bayar da hanyar inajin Dadin kasancewa dake a koda yaushe.


Karanta wannan >> Abubuwan da suke kawo mutuwar aure


12. Dake nakeson na Kare rayuwata dake nakeso na zauna har karshen rayuwata ina alfahari dake Rabin Raina a koda yaushe mukwana lafiya kiyi barci me Dadi.

13. Nagode da Irin kulawar da kike nunamin a kullum zamanmu a tare shine farincikina rashinki shi zai sanyani cikin halin bakinciki da damuwa ina fatan zakici gaba da bani kulawa.

14. Nazari na da tunanina a kullum Bai wuce akan yadda zakayi naga munyi aure ba ki Kira hakuri nasa kinyi Allah zai kawo mafita watarana zaki ganni a matsayin angonki kekuma amarya.

15. Daga lokacin Dana fara ganinki tunani na da komai ya tsaya babu abinda nake kallo a idona saike Koda rufe ido kuwa nayi hankalina Bai dawo jikina ba Saida na furta Miki ina sonki.

16. Yau da gobe akwana a tashi inata yankamiki filayen da suke cikin zuciya ta da alamu nanda wani lokaci zai zamto gabadaya ke kike da mallakin zuciya ta me kaunata nikuma zanyi farinciki da hakan.

17. Ina kuka a duk lokacin dana tuna da wata rana wacce zaki kirani Amma bazan amsaba ranar da numfashina ya Kare a duniya itace ranar rabuwa tun yanzu inajin wannan radadin a zuciya ta.

18. Ina Mai baki hakuri gimbiya ta kinkirani bana kusa kinmin massage bakiga reply ba hakan yabiyo bayane sakamakon rashin chaji a wayana nakai chaji kiyi hakuri ban fada Miki tun Farkon ba ina fatan zaki amshi uziri na.


Karanta wannan >> Waye yafi wani tsakanin nura m inuwa da Umar m Sharif.


19. Ni da kaina bansan irin soyayyar da nake Miki ba Kuma bansan adadinta ba idan Kuma kinaso kisan Irin soyayyar da nake Miki ki daga Kai da daddare ki irga yawan adadin taurarin da suke sama inda kin iya to soyyarki tanada adadi idan Kuma baki iya ba to soyayyarki batada adadi a zuciyata.

20. Nayi Miki alkawarin matukar ina raye bazaki taba kuka ba ni Zan share Miki hawaye bazan barki Kisha wahala ba Zan kula dake Kuma na rike alkawarin soyayyarmu.


Wannan munkawo Muku zafafan kalaman soyayya guda ashirin sannan muna Nan zamuci gaba ahakali zamuyitayi domin mu bayar da gudun mawarmu ga masoya.

Yakai Mai karantawa munaso kayi comment da Wanda yafi burgeka daga 1-20 hakanne zai Kara Mana kwarin gwiwa akan abinda muke mungode.


BAYANI AKAN ZAMAN AURE.

 
Kamar kullum yanda kuka sani muna kawo muku bayanai dakuma labarai akan abubuwan da suka shafi labarai, fasahar zamani , zamantakewa dukama filin girke-girke da sauran abubuwan da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullu.


Ayau munzo muku da bayani akan zaman aure dakuma hakkokin aure sakamakon yanayi da muka tsinci kanmu a wannan zamani Wanda zamu iya cewa yawancin abubuwan sun dauki hanyar lalacewa musamman a arewacin nigeria.


Menene aure ?.


Kusan zamu iya cewa kowan yasan menene aure Amma Kuma zamuyi bayani a gur-guje ma'ana da sauri- sauri sabida akwai inda nakeso muyi cikakken bayani akai shine wato zamantakewar aure Bayan anyi auren kenan.


Karanta wannan >> Yadda ake gurasa


Zamuyi bayanin yadda akeyin aure a arewacin nigeria ne sakamakon kowanne addini da yadda sukeyin nasu a fadin duniya kusan kowanne addini da al'adu suna yin aure Kuma yadda sukeyi ya banbanta.


Aure ana yinsa tsakanin namiji da mace domin su zama ma'aurata sannan Kuma dukkanin wani nauyi da yake kan iyayenta zan koma kan namijin ma'ana dukkanin wani Abu daya shafe ta to shiya shafa ciwonta yazama nashi haka Kuma dawainiyarta yazama nashi.


A takaice dai zamu iya cewa ita kanta matar tazama tashi Kuma halas dinsa zasu iya komai da junansu kundai gane manufarmu sannan kuma itama dole ta Kare hakkinsa ta biya masa bukarsa a duk lokacin daya nema.


Amma Kuma akwai wasu sharruda da sai namiji a cikasu kafin aure bawai haka kawai da kaga mace kace ka aureta ba wannan bahaka bane yanzu zamuyi muku cikakken bayanin abubuwan da ake bukata kafin aure da Wanda yazama wajibi dakum Wanda ake yi a al'adu.


Sadaki : Sadaki kusan zamu iya cewa shine ginshikin aure domin matukar babu sadaki to babu aure Amma Kuma zaka iya bayar da wani abu a matsayin sadaki kamar yadda tarihi yazo dashi kakanmu annabi Adam kafin a daura masa aure da hauwa'u da babu Kudi a lokacin sai yabarda zobensa aka daura musu.


Karanta wannan >> Yadda ake samosa


Abinda muke nufi dai tabbas sadaki dole ne Amma kuma a wannan lokacin ana bayarda kudi ne idan ma baka dashi wani a cikin abokananka ko danginka zasu biya maka dolene ne dai sai an bayar kafin a daura aure.


Gaisuwar uwa da uba : wannan wani kudine da ake kaiwa kafin aure  wajibi bane al'ada ce ta hausawa da akeyi tun zamanin kaka da kakanni zamu it cewa wannan kyautawa ne.


Goron sa Rana : Shima wanna idan za'asa ranar aurenne ake Kai goro da tabarma Amma Shima wannan a al'ada ne anakai goro da tabarma Amma yawanci a wannan lokacin an mayar da abun kamar dolene ana Raba goron ga tsofaffi da sauran mutane dai shine shaidar saka Rana.


Kafin ayi aure akwai sharruda nafarko dai a tabbatar tsakanin wadanda za'a daura ma auren sunada lafiya domin ba'a aure da mara lafiya sannan akwai ciyarwa, shayarwa, ilimantarwa, dakuma tufafi wadannan dolene bayan anyi aure.


Za'ayi taro da waliyyan amarya da waliyan ango ayi addu'a ayi komai sannan anayin taro gidan amaryar da gidan angon har wasu ma suyi walima da sauran abubuwa dai na nishadantarwa sabida murnar wannan auren.


Aure akwai iya adadin matan da aka kayyade wa mutum ya aura zai iya auren daga daya zuwa hudu Amma daganan shikenan aure Sunnah ne Kuma zaman ibada ne sai anyi hakuri Allah kabarmu da masoyanmu.


Zaman aure


Zaman aure wani shafi ne daban da rayuwar Dan Adam domin komai saiya banbanta Dana baya lokacin kana samartaka kokuma rayuwarki zata chanja daga yadda take da a gidan iyayenki angonki kokuma muce mijinki yazama garkuwarki daga wannan lokacin da aka daura muku aure.


Kaikuma namiji kazama magidanci iyali kaima zakayi don haka saika kula sosai Kuma ka kula da tarbiyyar matarka da iyalinka domin sun zama naka zaka fita kanemo sannan Kuma kazo ka Basu domin shine rayuwar auren.


Karanta wannan >> Jarumar kannywood Samira Ahmad tayi abin azo agani


Kekuma ke zaki kula dashi kiyi masa abinda zai faranta masa aduk lokacin da yake bukatarki yazama dole kije matutam kina lafiya babu abinda yake damunki sannan Kuma dole ku sirrinta sirrin junanku idan matsala ce kusan yadda zaku sasanta da junanku basai Kun fita anjiku ba.


Akwai kalubale da yawa kokuma muce jarabawa da ake jarabtarmu bayan aure ko kuga mijin yasamu raunin arziki sakamakon auren dayayi kokuma rikici tsakinin mata da mijin to dukkanin wadannan abubuwan sai anyi hakuri daga baya komai zai zama dai-dai domin za'a Saba.


Nan munyi muku bayani a takaice anan gaba Kuma zamuyj rubutu na musamman data matakin farko har karshe daga lokacin da kakeson yarinya da yadda zakayi har a daura muku aure ki jirayemu zuwa lokaci kadan.

YADDA AKE GURASA.


Sannunku dazuwa shafinmu na zazzauloaded sashen girke-girke muna fatan zaku kasance damu a kowacce rana a kowanne lokaci domin samun labarai da fanninka daban-daban na ilmantarwa.


Ayau munzo muku da bayanin yadda akeyin gurasa daga farko zuwa karshe tun daga lokacin da za'a kwaba ta har zuwa lokacin da za'aci ma'ana lokacin da za'a gama gaba dayanta don haka saiku natsu ku karanta dakyau.


Menene gurasa ?.


Gurasa wani nau'in abinci ne da ake gasashi sannan a kwadashi da kuli wasu Kuma sukan sanya masa miya suci ya danganta dai da yanayin yanda suke ci domin ba abinci bane na gida najeria kadai ba.


Karanta wannan >> Yadda ake samosa


Gurasa andade anayinta a duniya musamman a ksashen larabawa suna kiranta da (kubza) saidai tada ta bambanta data yanzu sakamakon da ana amfani da alkama yanzu Kuma akan sarrafa alkamar ne takoma fulawa sai ayi amfani da ita wajen yin abubuwa daban-daban dukkanin abinda alkama zatayi to yawanci fulawa ma zatayi.


Abubuwan da akeyin gurasa Basu da yawa idan kasamo fulawa da yeast shikenan saikuma ruwan sanyi Wanda zaka kwaba dashi, amfanin yeast din shi yake sata ta kumbura wasu sukan sanya ridi a samnata kadan wasu Kuma su barta haka.


Idan kuka samu baho wanda zaku kwaba aciki saiku zuba fulawan ku saka yeast aciki ku juya sosai saiku dauko wanna ruwan sanyin kuzuba aciki Amma saikunyi ahankali saboda kada ku cika ruwa anayinta da danko kamar yadda kike gani a hoto.

Bayannan Kuma sai maganar inda za'a gasa ta wasu suna amfani da kasko mai Fadi irin Wanda ake soya kwai saiku dorasa a wuta yayi zafi saiku dinga yaga Kuna sanyawa a kaskon har ta gasu saiku cire.


Karanta wannan >> Abubuwan da suke kawo mutuwar aure


Wasu Kuma suna amfani da tukunya mai kafa idan kuka Dora a murhu kuka hada wuta sosai sai ku sanya toka a cikin tukunyar kuzuba garwashin wuta a cikin tukunyar kunga dai kenan ciki da waje wuta saiku dinga yaga nanma Kuna likawa ta cikin tukunyar dayayi saiku cire.


Saikuma Wanda suke amfani da asalin tukunyar kasa wacce danan ita anyita ne sabida gasa gurasa Amma yawanci masuyin na sayarwa ne suke amfani da wanna ga irinta Nan a hoto kamar yadda kuke gani a kasa.

Angama kenan da yanda akeyin gurasar da yanda ake gasawa yanzu abu nagaba zamuyi muku bayani akan yadda zaku bandasata da kuli da man gyada kokuma damiya duk dai yanda kukaga damar yinta kowa da yanda yakeso.


Idan kuka dauko gurasar saiku ajiye a gefe saiku debo ruwa a cikin karamin Abu domin wanketa za'ayi idan kuka ajiye saiku dinga dauka Kuma sata Kuna wankewa da sauri sabida karta jike saiku samu faranti mai fadi kusa aciki ku barta.


Karanta wannan >> Waye yafi wani tsakanin nura m inuwa da Umar m sharif


Saiku siyo garin kuli kusanya magi da yaji dakuma gishiri aciki sannan Kuma ku soya man gyada ku tabbatar kunsa albasa aciki sabida yafi kamshi Amma Kuma idan man kuli ne shikena saiku bada kulin akan gurasar kusa Mai shikenan saici idan ma miyane haka.


Saikuma wadanda suke yanka kabeji da kokomba da sauran abubuwa dai irinsu tumatur da albasa duk Karin Dadi ne duk da dai bakowa keso ba Amma Wanda yakeso zai iya sanyawa.


Mungama da wanna darasin saikuma idan munkara haduwa a karo nagaba a wani darasin mungode da kasancewa damu sannan duk abinda baki fahinta ba saikuyi comment domin ayi muku Karin bayani.

YADDA AKE SAMOSA.

 
Barkanku dazuwa shafin zazzauloaded sashen girke-girke ayau munzo muku da sabon Abu kuma mai Dadi mai kayatarwa musamman a wajen hidimar biki, sauka ,walima kokuma taron siyasa da dukkanin wani waje da za'a ci abinci da sauransu.


Shi wannan Abu da muka zo muku dashi yanada sauki wajenyi kuma ko a gidanku zakuyishi batare da bukatan sai kaje wani kichin na musamman ba dukkanin abinda ake bukata a wannan Abu to tabbas za'a sameshi a gida.


Sunan wannan Abu da zamu koyar a yau shine (samosa) wasu mutane dayawa sunsanshi wasu kuma gaskiya suna ji ana yawan fadinsa Amma kuma basusan yanda zasuyi shi ba to yanzu dai zakuji yanda ake yinsa.


Menene samosa ?.


Samosa wani nau'in abinci ne kokuma muce (snacks) da akeyi da fulawa kuma a ci, samosa anayinsa a kasashen duniya daban-daban musamman kasar India birin Delhi suna yawan amafani dashi idan kaje gidajen cin abincinsu a wararen.


Abubuwan da akeyin samosa.


Kafin ka fara aikin samosa yakamata saika nemo dukkanin abubuwan da ake hadawa sannan kafara aikinka saboda gudun matsala karka fara Kuma kazo baka samu want abunba.


1. Fulawa.
2. Kwai.
3. Nama.
4 Maggi.
5. Kori.
6. Gishiri.
7. Mangyada.
8. Attarugu.
9. Albasa.
10. Karas.
11. Ruwa.
12. Baking powder.Wadannan abubuwan da muka lissafa guda goma sha biyu dai-dai sune akeyin samosa dasu, matukar kana bukatar samosanka yayi Dadi sosai to tabbas saika nemo wadannan abubjabu dana lissafa kafin kafara aikin ka.


Yadda ake hadawa.


Idan ka dauki fulawa kazuba a robanda zaka kwaba saika dauko kwai kafasa kazuba a ciki kasanya baking powader da gishiri kadan a ciki wasu sukan sanya magi a ciki Amma idan kanaso saika saka kadan idan kuma bakaso shikenan.


Tunda kasa gishiri dama amfaninsa saboda kar aji wannan fulawan salam-salam babu dandano ko kadan shiyasa muka zabi kasanya gishiri da magi Koda kadan-kadan ne.


Saika dauko ruwa kazuba ka kwabashi da karfi yafi na cin-cin ruwa yanda dai kasan idan ansashi a injin murza taliya zaiyi batare da wata matsala ba domin kunga idan yayi ruwa to bazaiyiwu ya niku a injin ba.


Bayan Kun kwaba shi zaikiu ajeshi a gefe ki dauko wannan naman ku wanke ku tafasa shi da magi da kori da gishiri idan ya tafasa saiku saukeshi ku jajjaga attarugu ku yanka albasa da magi ku zuba a cikin namannnan sauku nika shi ku aje a gefe.Wannan karas din shikuma saiku wanke ko samu abin goga karas ku gogashi kanana sosai saiku hada a cikin wannan naman ku juyashi sosai, wasu sunayi ko babu karas din Amma idan baku samuba zaku iyayinshi haka.


Bayan Kun gama saiku sa Mai kadan a kaskonku kuzuba wannan naman ku soyashi sama-sama karya soyu sosai saboda kunsan bayan an nadashi da wannan fulawan sai ankara soyawa.


Saiku dauko wannan fulawan da kuka kwaba saiku nikashi a injin taliya ku yankashi saiku dinga zuba naman aciki ki nade shi kamar yanda kuke gane a hoton da yake kasa.


Da zarar Kun gama duka sauku Dora man gyadanku a wuta idan yadau zafi saiku sa albasa saboda man gyadan yayi kamshi saiku dinga soya Wannan Wanda kuka nada.


Anan mukazo muku karshen wanna bayanin akan yadda ake samosa sai aje ayiwa ango domin yaci yaci Dadi, kamar dai kullum muna fada muku kuci gaba da kasancewa da wannan shafin namu dakuma sauran kafafen sadarwa mungode.

RAYUWAR KAYLOR NAVAS.

Rayuwar kaylor navas barka dazuwa wannan shafin namu kamar yanda muke Shirin sanar daku yau munzo muku da wani tsokaci ko want bangare daga rayuwar tauraron Golan Nan na psg Kuma tsohon Dan wasan real madrid da lavente Dan asalin kasar Costa Rica.


FARKON RAYUWAR KAYLOR NAVAS.


An haifi navas ashekarar 1986 awatan December nashekarar, navas nada mahaifiya maisuna sandra gamboa saikuma mahaifinshi maisuna fredy navas, mahaifan navas matalautane wanda tsananin talaucin yasanya suka kyale navas tunyana shekara 4tareda y'ar uwarsa dakuma kakanshi inda sukatafi neman kudi a iyakar kasar costarica da kasar amerika domin neman kudi dakuma abubuwan tafiyar da rayuwarsu cikin dadi.


Mahaifiyar navas tace wannan tafiya ce mai hatsarin gaske tareda rashin tabbas shiyasa muka kyale navas agida Amma azahirance kamata yayi mutafi dashi amma munyi nadamar wannan mataki damuka dauka injita kamar yadda tayi hira dawasu y'an jaridu ashekarun baya.


Tunbayan haihuwar navas mahaifinshi yanuna mashi soyayyar kwallon kafa bayan navas yacika shekara 5 aduniya sai yafara yin harkar wasanni inda y'ar uwarshi tayi amfani da kudin da akabarmasu agida tasanyashi wata makaranta maisuna pedregosso soccer inda yashare shekara 7 acikinta yana koyon harkar wasanni.


Sanyin jikin da navas kedashi shine yabashi matsala alokacin, Bayan kammmala karatun da yayi yarunka kokarin samun kungiyar dazairukama wasa amma duk inda yanema sai yarasa saboda bashida wani karsashi alokacin navas yayi sa'a inda alokqcin kungiyar deportivo saprissa takasar costarica tadaukeshi ashekarar 1995, yakwashe shekara 10 a kungiyar kuma yayi nasarar lashe kofuna 6 da kungiyar.


Kokarin da navas yayi yakama soyayyar mai kungiyar albacetes takasar spain wadda take a division 3 alokacin kuma yayi sa'a aka mika shi aro zuwa kumgiyar levente,kokarin da yanuna yasanya kungiyar levente sayen danwasan daga kungiyar albacetes akan kudi £100,000dollars .


Sayenda kungiyar levente tayimashi yasanya yafara buga gasar laliga ashekarar 2012 da levente kokarinshi yasanya kasarshi ta costarica kiran navas domin fara shirye-shiryen buga gasar world cup 2014. inda daganan tauraruwar danwasan tahasku aduniya kuma ashekarar yafara shiga jerin manyan gololi aduniya inda akemashi lakabi da bird ma'ana (tsuntsu).


Daya daga abinda y'an kasar costarica zasu iya tuna navas dashi shine kokarin da yayi agasar world cup na 2014 inda yayi namijin kokarin dasuka doke kasar uruguy daci 3_1 abinda yabaiwa duniya mamaki bayan irin manyan kwalllaayen dayakabe awasan yakuma taimaka kasartashi doke kasar greece abugun penalty kuma suka isa quater final nafarko atarihin kasar costarica.


Matukar kokarin da mai tsaron gidan yayi wato kaylor navas a world cup yasanya manyan kungiyoyi neman sayenshi sai dai Madrid tayi nasarar sayen danwasan daga kungiyar levente inda tabiya €10mlns euro wanda shine kudin fansar mai tsaro ragar a lokacin.


Navas yaxo Madrid ya iske casillas sai dai hakan bata bashi damar buga wasanni akai akai ba.Bayan tashi casillas Madrid taso tasiyo golan da zaimaye mata gurbin casillas saboda raahin yadda da kungiyar tanuna kan rashin sahihancin iya golar navas.


Zidane yatabbatar da cewar zaicigaba da amfani da navas donhaka baya bukatar wani gola wanda zai ajiye navas ba,
navas yayi kokari sosai tareda kafa tarihin da babu wani gola dayakafashi aduniya.navas yayi nasarar lashe kofin champion leangue 3 ajere wanda hakan yazama gola nafarko dayataba lashe kofin sau 3 ajere yakuma zama gola nafarko mafi karancin kwallaye aragarshi cikin kakar wasanni uku 3 agasar champion leangue.

Navas ya bayyana cewa zamana a real Madrid yabani damar sanin koni wanene aduniya wanda hakan yataimaka mani sosai wajen chanza rayuwar mahaifana dakuma nikaina,
navas cikakken christer ne kuma yakanyi adduar nan tacikin littafin Bible kafin ya shiga filin Wasa.


IYALAI.


Navas yahadu da matar daya aura ashekarar 2008 amma daman ba a budurwa ya auretaba kasancewar daman ta tabayin wani auren, sunan matar tashi fred salas sunada yara guda 2 mateo navas salas dakuma daniela navas salas.


Navas nada y'an uwa mata guda 3 wanda yanxu haka 1 fitacciyar mai gyaran gashice akasar costarica, kuma mai tsaron ragar ya yanke shawarar barin Madrid ne bayan yunkurin madrid na bentashi asanadiyyar kawo courtois shikuma Yana ganin hakan babban kalubale ne agareshi.


Kaylor navas yayi wani jawabi mai ratsa zuciya inda yake cewa zanbar Madrid ne dagangar jikina Amma zuciyata natareda Madrid har abada inji navas ajawabinshi nakarshe kafin yakoma p s g da taka ledarsa.

TARIHIN ALI NUHU.

 
Takaitaccen tarihin sarkin kannywood wato kungiyar shirya Fina-Finan hausa dake jihar kanon dabo, a yau abinda muka zo muku dashi kenan zamu gabatar muku Kuma muna fatan zaku kasance damu.


Ba iya tarihin rauwar wannan jarumi muka kawo muku ba, mun kawo muku harda irin nasarorin daya samu a rayuwa duk dai cewa mun kawo muku iya abinda muka Samu dangane da tarihin jarumin Kuma me shirya Fina-Finai Kuma sarki. Masana'antar kannywood.


Ali Nuhu Muhammad Wanda yawancin jama'a sukafi sani da (Sarki Ali Nuhu) an haifeshi ne a Ranar shabiyar (15), gawatan maris (march) shekara ta dubu daya da dari Tara da saba'in da hudu (1974) a garin maiduguri inda yanzu yakeda kusan shekara (46) a duniya.


Jarumin Dan asalin harin maiduguri ne inda yanzu haka ya koma jahar kano da zama yayinda wasu dayawa daga cikin mutane suke ta tunanin haifaffen jihar kano ne, wannan zance bahaka bane gaskiyar magana itace Dan maiduguri ne.


Be kasance a aiki guda daya ba dukda yana matsayin shugaba kokuma muce sarkin kannywood, yana harkar Fina-Finan turanci na kungiyar (Nollywood), sannan kuma yana shirya Fina-Finai tare dakuma bada umarni duk a cikin Shirin.


Ali Nuhu yanada dubban masoya idan mukayi duba da shafukansa na yanar gizo da suka hada da page dinsa na Facebook, Twitter da Kuma shafinsa na Instagram zamuga yadda yake da dubun masoya masu bibiyarsa a kids yaushe wadanda suka hada da hausawa da wadanda ba haisawa ba duk suna bibiyarsa.


A shafinsa na Twitter yanada mutane samada dubu dari da arba'in (140,000), saikuma shafinsa na Instagram samada mutum miliyan daya (1,000,000) sannan sai shafinsa na Facebook inda yakeda mabiya fiye da na ko'ina samada da mutum miliyan daya da dubu dari biyar (1,500,000) wadannan sune wadanda suke amfani da kafar sadarwa Banda sauran masoyansa da basa amfani da social media.


Jarumin Kuma me shirya Fina-Finai sannan me bada umarni wato Ali Nuhu yayi karatu tun daga matakin farko har zuwa jami'a inda bayan ya kammala karatunsa na secondary ya daura daga inda ya tsaya yayi karatun jami'ar ne a ( University of jos ) inda ya kammala yadawo yaci gaba da harkar Fina-Finan shi.


Zamu kawo muku kadan daga cikin Fina-Finan da jarumin yayi saboda yanzu babu lokacin da zamu kawo muku dukkanin wasu Fina-Finai da yayi sai dai daga baya zamu iya binciko muku su mu kawo muku su a wannan shafin namu.


KADAN DAGA CIKIN FINA-FINAN DA YAYI NA HAUSA.


1. Uwar miji.                 
2. Abin sirrine.
3. Ali.
4. Kasata.
5. Mu'amalat.
6. Abaya.
7. Alhini.
8. Zuwa da Kai.
9. Namijin duniya.
10. Ambato.
11. Ina mijina.
12. Masu aji.
13. Zo mu zauna.
14. Yanayi.
15. Mashi.
16. Gambiza.
17. Sakayya.
18. Harafin so.
19. Sangaya.
20. Ruhi.
21. Farin wata.
22. Gida da waje.
23. Bashin gaba.
24. Ragiwar yaki.
25. Jurwaye.
26. Kishin mata.
27. Khalid.
28. Umarnin uwa.
29. Raliya.
30. Bilal.2

                                         
Wadannan mun lissafo kadan ne daga cikin Fina-Finan da jarumin wato Ali Nuhu yayi a hausa saikuma yanzu zamu kawo muku kadan daga cikin Fina-Finan da yayi na turanci wato na Nollywood.


KADAN DAGA FINA-FINAN DAYAYI NA NOLLYWOOD.


1. Last flight to Abuja.
2. Blood and henna.
3. Confusion.
4. Newage network.                                           
5. Ojukoro.
6. Banana island ghost.


Duk Dan wasan baiyi Fina-Finan turanci dayawa ba yafiyin na hausa Amma Kuma ga gawurtattu Kuma fitattu guda shida daga cikin wadanda yayi Nan munkawo muku su.


Zamu iya cewa Ali Nuhu yana kan gaba wajen samun Nasarori daga cikin jaruman Fina-Finan hausa dakuma Fina-Finan turanci dayayi na Nollywood Suma ana zamu kawo muku kadan daga cikin nasarorin daya Samun tarihin rayuwarsa.


KADAN DAGA CIKIN NASARORIN DAYA SAMU.


1. Arewa Films Award (Best Actor).
2. 3rd Africa Movie Academy Awards
(Best Upcoming Actor award).
3. The Future Award (Best Actor).
4.ZuluAfricanFilmAcademyAwards(Best Actor).
5.Best of Nollywood Awards (Best Actor)(Hausa).
6. 9th Africa Movie Academy Awards (Best Supporting Actor).
7.Nigeria Entertainment Awards (Best Actor).
2013 2013 Best of Nollywood Awards Best Actor (Hausa) Nasara
8.City People Entertainment Awards (Kannywood Face).
9. Leadership Awards (Best Artist).
10. Arewa Music and Movie Awards.


Wadannan kadan ne daga cikin kyautuka (award) da sarkin kannywood wato ali nuhu yasamu Kuma haryanzu yana cigaba da samun kyautuka ma'ana yana film Kuma yana samu tauraruwarsa tana cigaba da haskawa a harkar Fina-Finai.


Anan zamu dakata saikuma ku jira rubutu nagaba da zamu kawo muku irin kalubalen daya Samu a rayuwa dakuma yawan iyalinsa da sauran abubuwan da bamuyi magana akamsu ba.

WAYE YAFI WANI TSAKANIN NURA M INUWA DA UMAR M SHARIF.

Assalamualaikum barkanku da wannan lokaci, ayau zamuyi tsokaci akan wadannan shahararrun Kuma fasihan mawakan hausa wadanda ake Kira da Nura M Inuwa dakuma abokin harhar tashi wato Umar M Sharif.


Mutane sun dade suna tambayar cewa acikinsu wanene yafi iya waka, kowa yasan wadannan mawaka sun kware Kuma sun shahara yanda ba'a tunani ba a iya fadin kasar nan ba har kasashen ketare dakuma kasashen mu na afirka.


To muma zamuyi iya abinda mukayi domin ganin mun kawo muku bambanci dake tsakaninsu dakuma takaitattun tarihinsu dakuma yanda suka fara waka da sauran abubuwa daya danganci rayuwar wadannan mawakan.


WANDA ZAMU FARA BAYANI AKAI SHINE UMAR M SHARIF.


Sunanshi shine Umar Muhammad Sharif Umar shine sunan da mahaifinsa malam Muhammad Sharif ya rada masa a rayuwarsa shikuma m din tana nufin Muhammad kenan shi baban umar din wato Muhammad Sharif.


Umar M Sharif haifaffen jihar kaduna ne Wanda daga baya harkarsa kokuma ince sana'arsa tasa yakoma Kano da rayuwa Wanda har wasu suke ganin kamar Dan Kano ne, to ba haka bane Dan kaduna ne.


Kuma shi wannan fasihin mawakin ba a iya waka ya tsaya ba ya kasance Dan kasuwa sannan Kuma jarumi a masana'antar shirya Fina-Finai ta kannywood dake cikin garin Kano.


Ya karbi kyaututtuka daban-daban a fagen wakoki dakuma Fina-Finai domin ya cancanta da wannan, yayi want fitacce shiri Wanda ya fito a jarumi sannan Kuma ya rera waka a cikin film din Wanda yana daya daga cikin abinda yasa darajar mawakin ta Kara sama a idon duniya, wato film din mariya.


An haifi Umar M Sharif a shakarar 1987 kuma yayi makaranta primary dakuma secondry a jihar tasa ta kaduna hayin rigasa, sannan Kuma yayi karatun addini dukda bamu kawo adadin yanda yayi ba domim karatun boko ya banbanta Dana addini.


DALILIN DAYASA YA FARA WAKA.


Umar ya bayyana want dalili dayayi sanadiyyar fara wakarsa da yakeyi har izuwa yanzu wanda wasu har dariya zasuyi idan sukaji wannan daili idan sukayi duba da yadda mawakin yayi fice a wakokin soyayya.


Yaci gaba dacewa a lokacin yana makarantar secondry ya kamu da soyayyar wata yarinya kyakkyawa Kuma yana sonta kwarai da gaske har cikin zuciyarsa sai rana daya ya fada ma abokansa abinda yake faruwa game da soyayyar da yakeyi ma wannan yarinyar.


Abin takaici a lokacin bai san soyayya ba baisan yadda akeyi ba shidai kawai yaji a ransa yana kaunar wannan yarinya, sukuma abokansa sai suka bashi shawarar yaje gidansu kawai idan tafito sai ya fada mata dukkanin abinda yake ransa, shikuma sai ya yarda da hakan.


Sai ya shirya wata rana da niyyar zaije gidansu yarinyar nan domin a Kira masa ita, bayan yaje kofar gidansu yarinyar sai yasamu wani yaro karami ya aikashi yace ya Kira masa ita a cikin gidan shikuma yaron yashiga kansa tsaye yace ana kiranta sai ta fito.


Shikuma Umar tunda yaji takun tafiyar yarinyar nan take sai gudu , badan komai yayi hakanba sai saboda tsoro a cikin ransa da razani domin shi lokacin ne na farko da ya taba zuwa wajen wata budurwa da sunan tadi, ita Kuma yarunyar tana karasowa taga bayanan saita juya ta koma cikin gida.


Haka Kuma ya Kara shiryowa domin yafada mata abinda yake ransa haka aka Kara maimaitawa tana fitowa saiya gudu, hakan yasa wannan yarinyar tagaji da wannan lamarin ta rasa waye yake mata wannan abun saiya aika Kuma ya gudu yarinyar taji haushi sosai.


Wata rana saiya Kara dawowa dai yana zuwa ya aika ita Kuma taki fitowa yaji shiru, shikuma a lokacin yayi kokarin ya daure ya fada mata domim a lokacin baiyi niyyar guduwa ba yayi niyyar ya dake dukda yanajin tsoro ya furta mata.


Hakanan Umar yatafi yana jin haushi a cikin ransa yana bakinciki yashiga damuwa sabida taki fitowa, kawai yana tafiya ya fara rera waka akan wannan al'amarin har yaje gidansu ,duk lokacin daya tuna sai yayita waka to akwai want abokin yayansa shikuma mawaki ne saiya bashi shawarar ya fara waka Kuma haka akayi sanadiyyar fara wakarsa kenan


MUN GAMA DA BAYANI AKAN UMAR M SHARIF YANZU ZAMU FARA NA NURA M INUWA.


Da farko dai sunansa Nura Musa Inuwa sunan sa na yanka Wanda mahaifinsa ya rada masa shine Nura shikuma mahaifinsa shine Musa Inuwa wannan dalilin ne yasa ake kiransa da Nura M Inuwa.


Shi Nura M Inuwa baya acting din film Amma Kuna yana oroducipr din film a masana'antar kannywood dake cikin jihar Kano sannan Kuma yana wakoki irin na film, siyasa, sarauta yakanyi wakokinnan ga mutane manyan mutane daban daban da suka hada da sarakai da sauran manyan mutane.


An haifi mawaki Nura M Inuwa a jihar Kano gwammaja karamar hukumar dala, sannan Nura M Inuwa yayi makaranta Shima yayi primary Kuma yayi secondry daga Nan Kuma ya dakata baici gaba ba Sai ya fadar hakar waka Wanda har yau yake cikinta.


Nura M Inuwa ya bayyana cewa Shi babu wani dalili kuma babu wanda yaja hankalinsa harya dara waka sannnan tun yana yaro karami haka kawai musamman idan an faranta masa Rai saiya zauna ya dinga rera waka yanajjn dadi a cikin ransa haka kuma idan aka bata masa rai sai yayi wakar ya huce haushinsa.


Yaci gaba dacewa tun baisan yanayin wakaba ko kalarta kokuma launi shidai kawai yanayi ne badan want abuba, saikuma daga baya yasa a ransa cewa zaiyi wakar da gaske yana girma har idan za'ayi maulidi ko wani babban taro a cikin makarantar tasu sai yayi waka yaje ya rera a wurin.


Shi Nura kamar yadda muka fada ba wakar addini ya fara ba idan kun tuna abinda muka fada a baya yanayi ne kawai domin jindadi, to idan ya kalli fill nafarko ko be kalla nabiyu ba saiyayi waka ta cigaban wanna film din yayita rerawa kawai yana jindadi tabbas yana kokari a wannan lokacin.


Haka-Haka dai yanayin wakoki tun baya zuwa Ana buga masa a studio har yafara zuwa to a wannann lokacin me yaga zai iya daukar wanna hanyar a matsayinka hanyar fadakarwa dakuma tura sakonni cikin sauki haka zalika ya dauketa a hanyar neman kudinsa.


WAKOKINSU DA SUKAYI FICE.


Umar m Sharif zamu dauki wakar mariya shikuma Nura m Inuwa zamu dauki wakar mai laya, wakar mariya tabbas tayi fice sosai haka Kuma wakar mailaya waka ce da tazo da wani sabon salo da rikitarwa domin yayi hausa iya hausa a wannan wakar Kuma itama tafito a want film me suna mailaya.


KALUBALEN DA SUKA FUSKANTA A RAYUWA.


Umar M sharif yasamu kalubale sanadiyyar wata yarinya data baro gidansu take wurinshi kaduna Wanda har yayi wakar "bako" idan ka saurara wakar duk zakaji abinda yafara Wanda har hakan yayi sanadiyyar zauwansa gidan yari.


Shikuma Nura M Inuwa tabbas yasamu babban kalubale Wanda zamu iya cewa yafi na Umar m Sharif sabida Shi an nemi a hallaka rauwarsa ne gabadaya yayinda wasu wadanda ake ta bincike domin a gano ko suwaye suka watsa masa "acid" a fusaka har yakai baya gani sosai sai da tubarau.


Yawan wakoki : zuwa yanzu bamu kayyade ba Amma Kuma zamu cigaba daga Nan inda muka dakata abinda zamuce shine kuci gaba da kasancewa da wannan shafin domin jin waye yafi want sannan wadannan irin nasarori suka samu dakuma wanda yafi samun kudi a harkar wakar.


ABUBUWAN DA SUKE KAWO MUTUWAR AURE.ABUBUWAN DA SUKE KAWO MUTUWAR AURE.Da farko barkanku da wannan lokaci fatan duk  kuna lafiya, kamar yanda kuka sani yau zamu  tattauna kuma zamuyi bayani akan abubuwan da suke kawo mutuwar.


Akwai abubuwan da suke  kawo mutuwar aure  dayawa amma kuma zamu bayyana wadanda sukafi karfi acikinsu.


Mutuwar aure ta yawaita musamman a wannan lokacin da muke  ciki kuma musamman a kasashen Hausa da bangarensu kamar arewacin Nigeria.


1. Karya.


Na farko shine karya domin a wannan lokacin maza sunfiye yaudarar mata da karya kafin su auresu domin suna tunanin wannan karyar ce  zatasa a auresu shiyasa suka zabi wannan bangare.


Kafin ayi aure  zakaga saurayi baya iya kashe ma kanshi dubu goma lokaci  daya  ba tareda wata damuwa ba, amma saikaga ya kashe wa  budurwa dubu ashirin.


Ita kuma zata kyautata zato akan cewa tun  yanzu kana mata wannan hidima Ina kuma ga anyi auren kaga kenan zatayi tunanin bayan anyi  auren abinda zaka mata yafi haka.


Abin takaici abin haushi sai bayan anyi  auren kaga komai ya tsaya abinda kake  mata da yanzu ka dema  mata tasaba kana kashe mata kudi yanzu taga shiru babu wani abin kirki.


Daga  karshe rigima ce  zata barke  a tsakaninku sai anta zuwa sulhu idan  anyi  sa' a komai yadawo dai-dai yanda akeso idan kuma an hadu da rashi hakuri shikenan sai aure  ya mutu don  haka akwai bukatar samari su rage wannan karyar kafin aure.


2. Rashin kaiwa munzalin aure.


Abu nabiyu kuma da yake  saurin kawo wannan babbar matsala ta saki wato mutuwar aure  shine kananun shekaru zakuga cewa yaro karami wanda  bai gama mallakar hankalin kansaba sai ya rikito aure.


Bawai muna nufin auren wuri babu dadi bane kuma ba muna nufin hakan bashida kyau ba tabbas auren wuri yanada kyau amma kuma aduba hankali kafin ayi.


Idan yazamto yanada kananun shekaru sannan baigama samun hankali da sanin rayuwarsa na balle ta wata tabbas babu fa'ida domin akan Abu kadan zasuyi fada yanzu zakaji yace na sakeki jeki gidanku.


To kunga wannan babbar matsala ce  domin karancin shekaru da rashin hankali ne  zaisashi ya aikata wannan domin saki halas ne  amma kuna ba'ason ayi, an bukaci kuje ayi muku sulhu har sai anga babu wata mafita da zata gyara lamarinku shine ake saki.


3. Rashin aikinyi.


Rashin aikinyi yana saga cikin many an dalilan da suke  kawo mutuwar aure domin kuwa bazai yiwu ka dauko yarinya daga gidan iyayenta ba ana bata ci da dasha sannan kai kazo ka ajeta da yunwa ba.Wannan wani babban kalubale ne ga matasa musamman a arewacin nigeria domin zakaga yaro bashida cikakkiyar sana'ar da zai rike kansa ma amma sai kuga ya nemo aure ya kamata mu daga mu nema sannan mu nemi aure ta yadda bazamubar iyalinmu da yunwa ba.Inda  zaka bar yarinya da yunwa babu abinci to tabbasa koda yaushe tana hangar gidansu ko makwafta kokuma gidan kawaye sukuna iyaye zasu bar yarsu tayita wahala ne ? kafa bazaiyiwuba dole kai daka ajiyeta kanema ka bata.


4. Yawo.Kalubale gareku mata domin wannan yawanci dabi'arku ne idan akace miji  bayanan kece shiganan fita nan to yana miki  fada bakyaji wata rana sekunsami matsala dashi  musamman idan kinada iyali.


Shi namiji a koda yaushe yanaso yaga matarsa acikin gida tana kulamai da iyali tana basu tarbiyya ta gari, sannan kuma yanaso a duk lokacin daya  fita  ya dawo ya ganki a gida.


Idan mijiki a fita  yadawo bai gankiba kuma baki fada masa  ba aka tareshi a gaya masa  kinga tun  an an zargi zai shiga zakaninku domin tunda har  kina iya fita  babu izininsa to komai ma zaki iyayi babu saninsa kenan.


Shiyasa idan har  kikasan mijinki bayason Abu to kekuma saiki kiyaye abinda zaisa kusami matsala idan har kina aikata masa  ba daidaiba kinga  kenan wata rana gidanku zaki koma domin a matsayinsa na mijinki tilas ne kimasa biyayya.


5. Rashin tsafta.

Rashin tsafata tsakaninku gabadaya daga matar har mijin ka iya haifar da matsala domin kunsan bakowa keson kazanta ba domin babu dadi, yakata kullum kiyi wanka bayan kin gama aiki shima kuma a lokacin da ya dawo aiki yayi wanka  tsaf.


Amma abin takaici saikaga mace tayi wasu kwananki ba wanka  ba kwalliya kokuma mijin babu wanka babu tsafta.


To idan daya  a cikinku bashida tsafa to tabbas indai ba'a gyara ba to za'a samu rabuwar hali domin ba kowa zai iya zama da kazama ba ko kazami domin iya tsafta tanada kyau a zamantakewa.


To anan  zamu dakata sai kuma idan munkawo muku cigaba idan Allah yayarda kudai kasance sa wannan shafin zazzauloaded a kullum domin karuwarku mungode.


Kalubale gareku mata domin wannan yawanci dabi'arku ne idan akace miji  bayanan kece shiganan fita nan to yana miki  fada bakyaji wata rana sekunsami matsala dashi  musamman idan kinada iyali.


Shi namiji a koda yaushe yanaso yaga matarsa acikin gida tana kulamai da iyali tana basu tarbiyya ta gari, sannan kuma yanaso a duk lokacin daya  fita  ya dawo ya ganki a gida.


Idan mijiki a fita  yadawo bai gankiba kuma baki fada masa  ba aka tareshi a gaya masa  kinga tun  an an zargi zai shiga zakaninku domin tunda har  kina iya fita  babu izininsa to komai ma zaki iyayi babu saninsa kenan.


Shiyasa idan har  kikasan mijinki bayason Abu to kekuma saiki kiyaye abinda zaisa kusami matsala idan har kina aikata masa  ba daidaiba kinga  kenan wata rana gidanku zaki koma domin a matsayinsa na mijinki tilas ne kimasa biyayya.


Kuma bawai iya mata bane masu wannan matsalar har mazan zakuga namiji idan yafita hira wajen abokai har sai tayi barci sannan zai dawo to wannan ba kyautawa bane domin kamata yayi ace karfe takwas zuwa Tara duk inda yake ya dawo wurin iyalinsa wannnan shine kyautawa.


6. Rashin kulawa.


Wasu dayawan mazaje zasu nunawa masoyiyarsu soyayya iya soyayya Amma da zarar anyi aure shikenan saikuga cewa wannan soyayyar gabadaya ya Dena nuna mata Kuma ya dena kulawa da ita Yanda ya kamata a cikin gidanshi.


Yakamata ace soyayyar da ka nuna mata a waje to idan tashigo gida ta tarar da wacce tafi wanna  domin a wannan lokacin ne ta zama taka mallakinka duk wani nauyinta ya sauka daga kan iyayenta ya dawo kanka a matsayinka na mijinta itakuma matarka.


To anan  zamu dakata sai kuma idan munkawo muku cigaba idan Allah yayarda kudai kasance sa wannan shafin zazzauloaded a kullum domin karuwarku idan Kuma kunada wata shawara ko abin cewa zaku iyayin comment.