Advertise On Nairanet

Header Ads

FARASHIN DATAR MTN A 2020.









FARASHIN DATAR MTN A 2020.


Assalam masu bibiyar shafinmu a koda yaushe muna muku fatan alkhairi fatan kuna lpy, kamar yanda muke a wannn lokacin.


A Yau kuma munzo muku da bayani akan farashin datar layin mtn a wanna lokacin sabida tambayoyi da muke gani da sakonnni.


Gaskiyar magana shine yanzu farashin datar layin mtn ta sauya daga yanda muka sani kamar yanda muka sani a baya sun bayar da offer kala-kala Amma kuma yanzu sun daina siyarwa.


A baya muna Siyan 1gb naira Dari biyu 200mb kuma naira hamsin Amma kuma wannan offer ne zuwa karshen March 2020 sannan akwai na welcome back data Shima offer ne kuma yanzu haka sun daina.


DATAR KULLUM.


1.N50 = 25MB

2.N100 = 75MB

3.N300 = 1GB .


Wannan shine farashin datar mtn ta kullum ma'ana ta tsawon awa 24 kenan, Amma kuma akwai irin wadda ake amfani da ita kwana biyu itama zamuyi bayani akai dakuma night browsing itama zamuyi bayani a Nan gaba.


Kuma yanda ake siya shine zaka danna *131# saika zaba duk wacce kakeson siya aciki.


DATAR KWANA BIYU.


1.200 = 200MB

2.500 = 2GB


Suma wadannan sune Wanda zakayi amfani dasu na tsawon kwana biyu daganan bazata sakeyin aiki ba domin ta Kare.


Itama yanda ake siya shine kamar dai na farkonnna *131# Amma kuma saika duba dakyau yanda zaka bambance ta kwana Daya dakuma ta kwana biyun.


DATAR SATI DAYA.


1.300 = 350MB

2.N500 = 1.5GB

3.1500 = 6GB

4.1000 = 2GB

5.500 = 1GB.


Wannan sune Wanda zakayi sati daya ma'ana kwana bakwai kana aiki dasu batare da want matsala ba indai ba ka karar da ita bane.


DATAR WATA DAYA.


1.N1000 = 1.5GB

2.N1200 = 2GB

3.N1500 = 3GB

4.N2000 = 4.5GB

5.N2500 = 6GB

6.3500 = 10GB

7.N5000 = 15GB

8.N10000 = 40GB

9.N15000 = 75GB

10.N20000 = 110GB


Kamar yadda kuka gani datar yananyin yawan wacce zaka siya yanayi saukin da zaka Samu ne domin yawan wacce zaka siya shine saukin itama zaka dannan *131# ne saika zabi (monthly) shine na tsawon wata Daya.


Kuma wannan datar ba sai kana want tsari bane zaka siya kawai indai mtn gareka to zance ya Kare domin zasu sayar maka duk wacce kake bukata acikinsu ko ta nawa ce.


Sannan akwai ta kwana uku wacce banyi bayani akanta ba Amma idan ka duba hoton zaka gani sannan kuma da wacce ake siya tare da katin waya itama duk zaka gani a hoto.

Post a Comment

0 Comments