Pr ads

Photography

Home JARUMAR KANNYWOOD SAMIRA AHMAD TAYI ABIN AZO AGANI.JARUMAR KANNYWOOD SAMIRA AHMAD TAYI ABIN AZO AGANI.Fitacciyar jarumar Fina-Finan hausa na masana'antar kannywood dake jihar kanon dabo, tayi abin azo agani kuma abinda ya burge jama'a sannan kuma abin a yaba mata ne duba da yadda tayi wannan namijin kokari.

Jarumar ta kannywood Mai suna Samira Ahmad tasa anyi famfo irinnan tuka-tuka a cikin makarantar da tayi ta gama ma'ana tsohuwar makarantar da tayi kuma ta gama a garin jogana.

Wannnan abin da tayi yafi ace ta  dauko Kudi ta baiwa malamai ko dalibai domin abune da daliban makarantar gaba  daya zasu amfana dashi su Bari har na bayansu Suma su amfana da wannan famfo da tayi a cikin makarantar.

Samira Ahmad tayi karatu a makarantar kuma ta kammala gabadaya a shekarar 2005, sannan kuma lokacin da tayi wannan makarantar tana Daya daga cikin dalibai masu ilimi da hazaka sosai a wannan makarantar.

Samira Ahmad tayiwa daliban da suke makarantar yanzu haka nasiha dakuma fadakarwa inda ta janyo hankalinsu akan taimakon makarantar zuwa Nan ganba, sannan ta fada musu cewa duk halinda suke ciki karsu manta da makarantar tasu.

Fitacciyar jarumar ta Fina-Finan kannywood wato Samira Ahmad tayi wannan tuka-tuka ne a tsohuwar makarantar tasu ta kwana ( Government Secondary School ) dake jogana a cikin jahar kano.

Samira Ahmad malama da sauran abokanan karatun nata sunyi shaidarta sosai akan iliminta kuma sunyi shaida akan kyawawan halayenta a makarantar kuma tanada kyauta tun tana dalibarta.

 A yayin da take gabatar da wannan aikin da tayi ta Kara janyo hankalin daliban na makarantar akan koda sunzama wani Abu karsu sake subar makarantar ta lalace su kula da ita sosai.


Taci gaba da cewa daya daga cikin manyan matsalolin da daliban makaranta indai ta kwana ce to matsalar itace ruwa ana yawan fuskantar wannan matsala a Koda yaushe domin ruwa shine abokin rayuwa.

Makarantar ta kwana dake joganan ta jihar Kano tana Daya daga cikin manyan makarantu na kwana da ake ji dasu kuma gwamnatin ta jihar tana kokarin gyara makarantar domin tana bukatar gyaran.

Wannan abunda wannan jaruma ta kannywood tayi ya kamata yazama madubi abun dubawa ga sauran jarumai na kannywood dakuma dukkanin wasu wadanda suka zama wani abu rayuwa.

Nan muka kawo muku karshen Labaran gabadaya saikuma idan munhadu daku a rubutu nagaba muna fatan zaku kasance da wannan shafin namu a koda yaushe.
No comments:
Write Comments