Pr ads

Photography

Home MAWAKAN HIP-HOP GUDA UKU DA SUKAYI FICE A AREWA.MAWAKAN HIP-HOP GUDA UKU DA SUKAYI FICE A AREWA.


Barkanku da zuwa wannan shafin namu na zazzauloaded shafin da yake  kawo muku labarai kala-kala sannan kuma yake baku damar Dora wakokinku idan kuna bukata.


A Yau dinnan muzo muku da wasu shahararrun mawakan hip-hop da sukayi fice a arewacin nigeria, kuma ba a iya kasar Nan ake sauraron wakokinsu ba ana sauraronsu har a kasashen ketare.


Kasashen sun hada da kamaru, gana, nijar, sudan, chadi dakum sauran kasashen da suke nashiyar Africa duk ana sauraron wakokinsu.


Zamu kawo muku sunansu hade da shekarunsu dakuma inda aka haifesu ma'ana asalinsu dakuma inda suke rayuwa dakuma wakokinsu da sukayi fice sosai ake saurara.


Sanin kowa ne cewa suna amfani da harshen hausa ne wahen rera wakar ba wani yare da daban ba Amma kuma sukan hada da turanci wani lokacin sabida abin yafi tafiya cikin tsari kuma da dadi wajen ambatawa.


1.DJ AB


Mawaki dj ab Dan kungiyar Yns (Yaran North Side ) Sanin kowa ne dj ab yayi suna sosai a kasar mu ta Nigeria dakuma sauran kasashe domin yanada matukar fasaha wajen rap yayi matukar kwarewa sosai sannan kuma bugu da Kari ya Dade yanayi kuma haryanzu yana kan ganiyarsa domin haryanzu yana sakin sababbin wakoki.


Ya lashe kyautuka daban daban dakuma lambar yabo a tarihin rauwarsa inda yayi wakoki wadanda sukayi suna sosai.


Dj ab saurayi ne kokuma ince matashi Wanda haryanzu yana kararu bairiga ya kammala ba Amma haryanzu yana wakarsa abin burgewa kuma yana karatunsa.


Yunkurinsa yanzu shine yana kokarin yin wakoki da manyan mawaka na kudu irinsu young6ix Mr easi dakuma wakar da zasu fitar Wanda yayi featuring din Zlatan da abokinsa Rahman jago.


SUNA = Haruna Abdullahi.

GARI = Kaduna.

LAKABI = Dj Abba.

SHEKARU = 28 December 1993.

WAKOKI MAFI SHAHARA = Totally, Soyayya dakuma Kumatu.


2.B O C


Boc madaki shine nabiyu mawaki ne dayayi fice wajen hausa tsantsa domin yanada baiwa wajen sarrafa harshensa gakuma Karin magana.


Mutane manya da yara suna son sauraron wakokinsa sabida hausarsa ba kowace kalma bace boc zai fada kasamu bahaushe a fassara maka ita ba yanda take.


Boc madaki yayi wakoki masu zafi da sukasa shi yayi suna sannan yati featuring na wasu manya mawaka hakan yasa darajar mawakin yayi sama sosai.


Haka kuma Shima ya lashe kyauta kala-kala a shekarun da yayi yana rera waka a cikin rayuwarsa.


SUNA = Luka Bulus.

GARI = Bauchi.

LAKABI = Barde Ogan Casu.

WAKOKI MAFI SHAHARA = Zafi, Dan Gaye dakuma Labarbaru.


3.CLASSIQ.


Mawaki Classiq tauraruwarsa tayi matukar haskawa saidai kuma daga baya abubuwan nasa sunja baya, Amma hakan ba yana nufin yabar harkar waka bane.


Classiq yayi fice musamman lokacin da ya saki wakarsa me suna (Anfara) gayu sunyishi sosai a lokacin sakamakon irin yadda wakar ta fita sosai kuma ya sake video dinta inda video yayi matukar baiwa mutane mamaki domin kyau din da video din yayi, saboda sunyi wanka me kyau a wakar.


Classiq yayi waka da manyan mutane irinsu (MI) dakuma sauransu , yazagaya wuri daban-daban domin bunkasa harkarsa saidai bai tsaya wuri Daya ba.


Yasamu nasarori daban daban musamma daga 2015 zuwa 2018 ya taka rawar gani kwarai da gaske kuma yayi kokari tun yana matashinsa.


SUNA = Buba Barnabas Luka.

GARI = Bauchi.

LAKABI = Arewa mafia.

RANAR HAIHUWA = 21 September 1991.

WAKOKI MAFI SHAHARA = Anfara, Zauna dakuma Juya.

Kuci gaba da ziyarar wanna shafin domin samun wakoki dakuma tarihin mawaka dakuma rayuwarsu.
No comments:
Write Comments