Pr ads

Photography

Home ABUBUWAN DA SUKE KAWO MUTUWAR AURE.ABUBUWAN DA SUKE KAWO MUTUWAR AURE.Da farko barkanku da wannan lokaci fatan duk  kuna lafiya, kamar yanda kuka sani yau zamu  tattauna kuma zamuyi bayani akan abubuwan da suke kawo mutuwar.


Akwai abubuwan da suke  kawo mutuwar aure  dayawa amma kuma zamu bayyana wadanda sukafi karfi acikinsu.


Mutuwar aure ta yawaita musamman a wannan lokacin da muke  ciki kuma musamman a kasashen Hausa da bangarensu kamar arewacin Nigeria.


1. Karya.


Na farko shine karya domin a wannan lokacin maza sunfiye yaudarar mata da karya kafin su auresu domin suna tunanin wannan karyar ce  zatasa a auresu shiyasa suka zabi wannan bangare.


Kafin ayi aure  zakaga saurayi baya iya kashe ma kanshi dubu goma lokaci  daya  ba tareda wata damuwa ba, amma saikaga ya kashe wa  budurwa dubu ashirin.


Ita kuma zata kyautata zato akan cewa tun  yanzu kana mata wannan hidima Ina kuma ga anyi auren kaga kenan zatayi tunanin bayan anyi  auren abinda zaka mata yafi haka.


Abin takaici abin haushi sai bayan anyi  auren kaga komai ya tsaya abinda kake  mata da yanzu ka dema  mata tasaba kana kashe mata kudi yanzu taga shiru babu wani abin kirki.


Daga  karshe rigima ce  zata barke  a tsakaninku sai anta zuwa sulhu idan  anyi  sa' a komai yadawo dai-dai yanda akeso idan kuma an hadu da rashi hakuri shikenan sai aure  ya mutu don  haka akwai bukatar samari su rage wannan karyar kafin aure.


2. Rashin kaiwa munzalin aure.


Abu nabiyu kuma da yake  saurin kawo wannan babbar matsala ta saki wato mutuwar aure  shine kananun shekaru zakuga cewa yaro karami wanda  bai gama mallakar hankalin kansaba sai ya rikito aure.


Bawai muna nufin auren wuri babu dadi bane kuma ba muna nufin hakan bashida kyau ba tabbas auren wuri yanada kyau amma kuma aduba hankali kafin ayi.


Idan yazamto yanada kananun shekaru sannan baigama samun hankali da sanin rayuwarsa na balle ta wata tabbas babu fa'ida domin akan Abu kadan zasuyi fada yanzu zakaji yace na sakeki jeki gidanku.


To kunga wannan babbar matsala ce  domin karancin shekaru da rashin hankali ne  zaisashi ya aikata wannan domin saki halas ne  amma kuna ba'ason ayi, an bukaci kuje ayi muku sulhu har sai anga babu wata mafita da zata gyara lamarinku shine ake saki.


3. Rashin aikinyi.


Rashin aikinyi yana saga cikin many an dalilan da suke  kawo mutuwar aure domin kuwa bazai yiwu ka dauko yarinya daga gidan iyayenta ba ana bata ci da dasha sannan kai kazo ka ajeta da yunwa ba.Wannan wani babban kalubale ne ga matasa musamman a arewacin nigeria domin zakaga yaro bashida cikakkiyar sana'ar da zai rike kansa ma amma sai kuga ya nemo aure ya kamata mu daga mu nema sannan mu nemi aure ta yadda bazamubar iyalinmu da yunwa ba.Inda  zaka bar yarinya da yunwa babu abinci to tabbasa koda yaushe tana hangar gidansu ko makwafta kokuma gidan kawaye sukuna iyaye zasu bar yarsu tayita wahala ne ? kafa bazaiyiwuba dole kai daka ajiyeta kanema ka bata.


4. Yawo.Kalubale gareku mata domin wannan yawanci dabi'arku ne idan akace miji  bayanan kece shiganan fita nan to yana miki  fada bakyaji wata rana sekunsami matsala dashi  musamman idan kinada iyali.


Shi namiji a koda yaushe yanaso yaga matarsa acikin gida tana kulamai da iyali tana basu tarbiyya ta gari, sannan kuma yanaso a duk lokacin daya  fita  ya dawo ya ganki a gida.


Idan mijiki a fita  yadawo bai gankiba kuma baki fada masa  ba aka tareshi a gaya masa  kinga tun  an an zargi zai shiga zakaninku domin tunda har  kina iya fita  babu izininsa to komai ma zaki iyayi babu saninsa kenan.


Shiyasa idan har  kikasan mijinki bayason Abu to kekuma saiki kiyaye abinda zaisa kusami matsala idan har kina aikata masa  ba daidaiba kinga  kenan wata rana gidanku zaki koma domin a matsayinsa na mijinki tilas ne kimasa biyayya.


5. Rashin tsafta.

Rashin tsafata tsakaninku gabadaya daga matar har mijin ka iya haifar da matsala domin kunsan bakowa keson kazanta ba domin babu dadi, yakata kullum kiyi wanka bayan kin gama aiki shima kuma a lokacin da ya dawo aiki yayi wanka  tsaf.


Amma abin takaici saikaga mace tayi wasu kwananki ba wanka  ba kwalliya kokuma mijin babu wanka babu tsafta.


To idan daya  a cikinku bashida tsafa to tabbas indai ba'a gyara ba to za'a samu rabuwar hali domin ba kowa zai iya zama da kazama ba ko kazami domin iya tsafta tanada kyau a zamantakewa.


To anan  zamu dakata sai kuma idan munkawo muku cigaba idan Allah yayarda kudai kasance sa wannan shafin zazzauloaded a kullum domin karuwarku mungode.


Kalubale gareku mata domin wannan yawanci dabi'arku ne idan akace miji  bayanan kece shiganan fita nan to yana miki  fada bakyaji wata rana sekunsami matsala dashi  musamman idan kinada iyali.


Shi namiji a koda yaushe yanaso yaga matarsa acikin gida tana kulamai da iyali tana basu tarbiyya ta gari, sannan kuma yanaso a duk lokacin daya  fita  ya dawo ya ganki a gida.


Idan mijiki a fita  yadawo bai gankiba kuma baki fada masa  ba aka tareshi a gaya masa  kinga tun  an an zargi zai shiga zakaninku domin tunda har  kina iya fita  babu izininsa to komai ma zaki iyayi babu saninsa kenan.


Shiyasa idan har  kikasan mijinki bayason Abu to kekuma saiki kiyaye abinda zaisa kusami matsala idan har kina aikata masa  ba daidaiba kinga  kenan wata rana gidanku zaki koma domin a matsayinsa na mijinki tilas ne kimasa biyayya.


Kuma bawai iya mata bane masu wannan matsalar har mazan zakuga namiji idan yafita hira wajen abokai har sai tayi barci sannan zai dawo to wannan ba kyautawa bane domin kamata yayi ace karfe takwas zuwa Tara duk inda yake ya dawo wurin iyalinsa wannnan shine kyautawa.


6. Rashin kulawa.


Wasu dayawan mazaje zasu nunawa masoyiyarsu soyayya iya soyayya Amma da zarar anyi aure shikenan saikuga cewa wannan soyayyar gabadaya ya Dena nuna mata Kuma ya dena kulawa da ita Yanda ya kamata a cikin gidanshi.


Yakamata ace soyayyar da ka nuna mata a waje to idan tashigo gida ta tarar da wacce tafi wanna  domin a wannan lokacin ne ta zama taka mallakinka duk wani nauyinta ya sauka daga kan iyayenta ya dawo kanka a matsayinka na mijinta itakuma matarka.


To anan  zamu dakata sai kuma idan munkawo muku cigaba idan Allah yayarda kudai kasance sa wannan shafin zazzauloaded a kullum domin karuwarku idan Kuma kunada wata shawara ko abin cewa zaku iyayin comment.
1 comment:
Write Comments