Pr ads

Photography

Home RAYUWAR KAYLOR NAVAS.

Rayuwar kaylor navas barka dazuwa wannan shafin namu kamar yanda muke Shirin sanar daku yau munzo muku da wani tsokaci ko want bangare daga rayuwar tauraron Golan Nan na psg Kuma tsohon Dan wasan real madrid da lavente Dan asalin kasar Costa Rica.


FARKON RAYUWAR KAYLOR NAVAS.


An haifi navas ashekarar 1986 awatan December nashekarar, navas nada mahaifiya maisuna sandra gamboa saikuma mahaifinshi maisuna fredy navas, mahaifan navas matalautane wanda tsananin talaucin yasanya suka kyale navas tunyana shekara 4tareda y'ar uwarsa dakuma kakanshi inda sukatafi neman kudi a iyakar kasar costarica da kasar amerika domin neman kudi dakuma abubuwan tafiyar da rayuwarsu cikin dadi.


Mahaifiyar navas tace wannan tafiya ce mai hatsarin gaske tareda rashin tabbas shiyasa muka kyale navas agida Amma azahirance kamata yayi mutafi dashi amma munyi nadamar wannan mataki damuka dauka injita kamar yadda tayi hira dawasu y'an jaridu ashekarun baya.


Tunbayan haihuwar navas mahaifinshi yanuna mashi soyayyar kwallon kafa bayan navas yacika shekara 5 aduniya sai yafara yin harkar wasanni inda y'ar uwarshi tayi amfani da kudin da akabarmasu agida tasanyashi wata makaranta maisuna pedregosso soccer inda yashare shekara 7 acikinta yana koyon harkar wasanni.


Sanyin jikin da navas kedashi shine yabashi matsala alokacin, Bayan kammmala karatun da yayi yarunka kokarin samun kungiyar dazairukama wasa amma duk inda yanema sai yarasa saboda bashida wani karsashi alokacin navas yayi sa'a inda alokqcin kungiyar deportivo saprissa takasar costarica tadaukeshi ashekarar 1995, yakwashe shekara 10 a kungiyar kuma yayi nasarar lashe kofuna 6 da kungiyar.


Kokarin da navas yayi yakama soyayyar mai kungiyar albacetes takasar spain wadda take a division 3 alokacin kuma yayi sa'a aka mika shi aro zuwa kumgiyar levente,kokarin da yanuna yasanya kungiyar levente sayen danwasan daga kungiyar albacetes akan kudi £100,000dollars .


Sayenda kungiyar levente tayimashi yasanya yafara buga gasar laliga ashekarar 2012 da levente kokarinshi yasanya kasarshi ta costarica kiran navas domin fara shirye-shiryen buga gasar world cup 2014. inda daganan tauraruwar danwasan tahasku aduniya kuma ashekarar yafara shiga jerin manyan gololi aduniya inda akemashi lakabi da bird ma'ana (tsuntsu).


Daya daga abinda y'an kasar costarica zasu iya tuna navas dashi shine kokarin da yayi agasar world cup na 2014 inda yayi namijin kokarin dasuka doke kasar uruguy daci 3_1 abinda yabaiwa duniya mamaki bayan irin manyan kwalllaayen dayakabe awasan yakuma taimaka kasartashi doke kasar greece abugun penalty kuma suka isa quater final nafarko atarihin kasar costarica.


Matukar kokarin da mai tsaron gidan yayi wato kaylor navas a world cup yasanya manyan kungiyoyi neman sayenshi sai dai Madrid tayi nasarar sayen danwasan daga kungiyar levente inda tabiya €10mlns euro wanda shine kudin fansar mai tsaro ragar a lokacin.


Navas yaxo Madrid ya iske casillas sai dai hakan bata bashi damar buga wasanni akai akai ba.Bayan tashi casillas Madrid taso tasiyo golan da zaimaye mata gurbin casillas saboda raahin yadda da kungiyar tanuna kan rashin sahihancin iya golar navas.


Zidane yatabbatar da cewar zaicigaba da amfani da navas donhaka baya bukatar wani gola wanda zai ajiye navas ba,
navas yayi kokari sosai tareda kafa tarihin da babu wani gola dayakafashi aduniya.navas yayi nasarar lashe kofin champion leangue 3 ajere wanda hakan yazama gola nafarko dayataba lashe kofin sau 3 ajere yakuma zama gola nafarko mafi karancin kwallaye aragarshi cikin kakar wasanni uku 3 agasar champion leangue.

Navas ya bayyana cewa zamana a real Madrid yabani damar sanin koni wanene aduniya wanda hakan yataimaka mani sosai wajen chanza rayuwar mahaifana dakuma nikaina,
navas cikakken christer ne kuma yakanyi adduar nan tacikin littafin Bible kafin ya shiga filin Wasa.


IYALAI.


Navas yahadu da matar daya aura ashekarar 2008 amma daman ba a budurwa ya auretaba kasancewar daman ta tabayin wani auren, sunan matar tashi fred salas sunada yara guda 2 mateo navas salas dakuma daniela navas salas.


Navas nada y'an uwa mata guda 3 wanda yanxu haka 1 fitacciyar mai gyaran gashice akasar costarica, kuma mai tsaron ragar ya yanke shawarar barin Madrid ne bayan yunkurin madrid na bentashi asanadiyyar kawo courtois shikuma Yana ganin hakan babban kalubale ne agareshi.


Kaylor navas yayi wani jawabi mai ratsa zuciya inda yake cewa zanbar Madrid ne dagangar jikina Amma zuciyata natareda Madrid har abada inji navas ajawabinshi nakarshe kafin yakoma p s g da taka ledarsa.

No comments:
Write Comments