Pr ads

Photography

Home TARIHIN ALI NUHU.

Takaitaccen tarihin sarkin kannywood wato kungiyar shirya Fina-Finan hausa dake jihar kanon dabo, a yau abinda muka zo muku dashi kenan zamu gabatar muku Kuma muna fatan zaku kasance damu.


Ba iya tarihin rauwar wannan jarumi muka kawo muku ba, mun kawo muku harda irin nasarorin daya samu a rayuwa duk dai cewa mun kawo muku iya abinda muka Samu dangane da tarihin jarumin Kuma me shirya Fina-Finai Kuma sarki. Masana'antar kannywood.


Ali Nuhu Muhammad Wanda yawancin jama'a sukafi sani da (Sarki Ali Nuhu) an haifeshi ne a Ranar shabiyar (15), gawatan maris (march) shekara ta dubu daya da dari Tara da saba'in da hudu (1974) a garin maiduguri inda yanzu yakeda kusan shekara (46) a duniya.


Jarumin Dan asalin harin maiduguri ne inda yanzu haka ya koma jahar kano da zama yayinda wasu dayawa daga cikin mutane suke ta tunanin haifaffen jihar kano ne, wannan zance bahaka bane gaskiyar magana itace Dan maiduguri ne.


Be kasance a aiki guda daya ba dukda yana matsayin shugaba kokuma muce sarkin kannywood, yana harkar Fina-Finan turanci na kungiyar (Nollywood), sannan kuma yana shirya Fina-Finai tare dakuma bada umarni duk a cikin Shirin.


Ali Nuhu yanada dubban masoya idan mukayi duba da shafukansa na yanar gizo da suka hada da page dinsa na Facebook, Twitter da Kuma shafinsa na Instagram zamuga yadda yake da dubun masoya masu bibiyarsa a kids yaushe wadanda suka hada da hausawa da wadanda ba haisawa ba duk suna bibiyarsa.


A shafinsa na Twitter yanada mutane samada dubu dari da arba'in (140,000), saikuma shafinsa na Instagram samada mutum miliyan daya (1,000,000) sannan sai shafinsa na Facebook inda yakeda mabiya fiye da na ko'ina samada da mutum miliyan daya da dubu dari biyar (1,500,000) wadannan sune wadanda suke amfani da kafar sadarwa Banda sauran masoyansa da basa amfani da social media.


Jarumin Kuma me shirya Fina-Finai sannan me bada umarni wato Ali Nuhu yayi karatu tun daga matakin farko har zuwa jami'a inda bayan ya kammala karatunsa na secondary ya daura daga inda ya tsaya yayi karatun jami'ar ne a ( University of jos ) inda ya kammala yadawo yaci gaba da harkar Fina-Finan shi.


Zamu kawo muku kadan daga cikin Fina-Finan da jarumin yayi saboda yanzu babu lokacin da zamu kawo muku dukkanin wasu Fina-Finai da yayi sai dai daga baya zamu iya binciko muku su mu kawo muku su a wannan shafin namu.


KADAN DAGA CIKIN FINA-FINAN DA YAYI NA HAUSA.


1. Uwar miji.                 
2. Abin sirrine.
3. Ali.
4. Kasata.
5. Mu'amalat.
6. Abaya.
7. Alhini.
8. Zuwa da Kai.
9. Namijin duniya.
10. Ambato.
11. Ina mijina.
12. Masu aji.
13. Zo mu zauna.
14. Yanayi.
15. Mashi.
16. Gambiza.
17. Sakayya.
18. Harafin so.
19. Sangaya.
20. Ruhi.
21. Farin wata.
22. Gida da waje.
23. Bashin gaba.
24. Ragiwar yaki.
25. Jurwaye.
26. Kishin mata.
27. Khalid.
28. Umarnin uwa.
29. Raliya.
30. Bilal.2

                                         
Wadannan mun lissafo kadan ne daga cikin Fina-Finan da jarumin wato Ali Nuhu yayi a hausa saikuma yanzu zamu kawo muku kadan daga cikin Fina-Finan da yayi na turanci wato na Nollywood.


KADAN DAGA FINA-FINAN DAYAYI NA NOLLYWOOD.


1. Last flight to Abuja.
2. Blood and henna.
3. Confusion.
4. Newage network.                                           
5. Ojukoro.
6. Banana island ghost.


Duk Dan wasan baiyi Fina-Finan turanci dayawa ba yafiyin na hausa Amma Kuma ga gawurtattu Kuma fitattu guda shida daga cikin wadanda yayi Nan munkawo muku su.


Zamu iya cewa Ali Nuhu yana kan gaba wajen samun Nasarori daga cikin jaruman Fina-Finan hausa dakuma Fina-Finan turanci dayayi na Nollywood Suma ana zamu kawo muku kadan daga cikin nasarorin daya Samun tarihin rayuwarsa.


KADAN DAGA CIKIN NASARORIN DAYA SAMU.


1. Arewa Films Award (Best Actor).
2. 3rd Africa Movie Academy Awards
(Best Upcoming Actor award).
3. The Future Award (Best Actor).
4.ZuluAfricanFilmAcademyAwards(Best Actor).
5.Best of Nollywood Awards (Best Actor)(Hausa).
6. 9th Africa Movie Academy Awards (Best Supporting Actor).
7.Nigeria Entertainment Awards (Best Actor).
2013 2013 Best of Nollywood Awards Best Actor (Hausa) Nasara
8.City People Entertainment Awards (Kannywood Face).
9. Leadership Awards (Best Artist).
10. Arewa Music and Movie Awards.


Wadannan kadan ne daga cikin kyautuka (award) da sarkin kannywood wato ali nuhu yasamu Kuma haryanzu yana cigaba da samun kyautuka ma'ana yana film Kuma yana samu tauraruwarsa tana cigaba da haskawa a harkar Fina-Finai.


Anan zamu dakata saikuma ku jira rubutu nagaba da zamu kawo muku irin kalubalen daya Samu a rayuwa dakuma yawan iyalinsa da sauran abubuwan da bamuyi magana akamsu ba.
No comments:
Write Comments