Pr ads

Photography

Home BAYANI AKAN ZAMAN AURE.

Kamar kullum yanda kuka sani muna kawo muku bayanai dakuma labarai akan abubuwan da suka shafi labarai, fasahar zamani , zamantakewa dukama filin girke-girke da sauran abubuwan da suka shafi rayuwarmu ta yau da kullu.


Ayau munzo muku da bayani akan zaman aure dakuma hakkokin aure sakamakon yanayi da muka tsinci kanmu a wannan zamani Wanda zamu iya cewa yawancin abubuwan sun dauki hanyar lalacewa musamman a arewacin nigeria.


Menene aure ?.


Kusan zamu iya cewa kowan yasan menene aure Amma Kuma zamuyi bayani a gur-guje ma'ana da sauri- sauri sabida akwai inda nakeso muyi cikakken bayani akai shine wato zamantakewar aure Bayan anyi auren kenan.


Karanta wannan >> Yadda ake gurasa


Zamuyi bayanin yadda akeyin aure a arewacin nigeria ne sakamakon kowanne addini da yadda sukeyin nasu a fadin duniya kusan kowanne addini da al'adu suna yin aure Kuma yadda sukeyi ya banbanta.


Aure ana yinsa tsakanin namiji da mace domin su zama ma'aurata sannan Kuma dukkanin wani nauyi da yake kan iyayenta zan koma kan namijin ma'ana dukkanin wani Abu daya shafe ta to shiya shafa ciwonta yazama nashi haka Kuma dawainiyarta yazama nashi.


A takaice dai zamu iya cewa ita kanta matar tazama tashi Kuma halas dinsa zasu iya komai da junansu kundai gane manufarmu sannan kuma itama dole ta Kare hakkinsa ta biya masa bukarsa a duk lokacin daya nema.


Amma Kuma akwai wasu sharruda da sai namiji a cikasu kafin aure bawai haka kawai da kaga mace kace ka aureta ba wannan bahaka bane yanzu zamuyi muku cikakken bayanin abubuwan da ake bukata kafin aure da Wanda yazama wajibi dakum Wanda ake yi a al'adu.


Sadaki : Sadaki kusan zamu iya cewa shine ginshikin aure domin matukar babu sadaki to babu aure Amma Kuma zaka iya bayar da wani abu a matsayin sadaki kamar yadda tarihi yazo dashi kakanmu annabi Adam kafin a daura masa aure da hauwa'u da babu Kudi a lokacin sai yabarda zobensa aka daura musu.


Karanta wannan >> Yadda ake samosa


Abinda muke nufi dai tabbas sadaki dole ne Amma kuma a wannan lokacin ana bayarda kudi ne idan ma baka dashi wani a cikin abokananka ko danginka zasu biya maka dolene ne dai sai an bayar kafin a daura aure.


Gaisuwar uwa da uba : wannan wani kudine da ake kaiwa kafin aure  wajibi bane al'ada ce ta hausawa da akeyi tun zamanin kaka da kakanni zamu it cewa wannan kyautawa ne.


Goron sa Rana : Shima wanna idan za'asa ranar aurenne ake Kai goro da tabarma Amma Shima wannan a al'ada ne anakai goro da tabarma Amma yawanci a wannan lokacin an mayar da abun kamar dolene ana Raba goron ga tsofaffi da sauran mutane dai shine shaidar saka Rana.


Kafin ayi aure akwai sharruda nafarko dai a tabbatar tsakanin wadanda za'a daura ma auren sunada lafiya domin ba'a aure da mara lafiya sannan akwai ciyarwa, shayarwa, ilimantarwa, dakuma tufafi wadannan dolene bayan anyi aure.


Za'ayi taro da waliyyan amarya da waliyan ango ayi addu'a ayi komai sannan anayin taro gidan amaryar da gidan angon har wasu ma suyi walima da sauran abubuwa dai na nishadantarwa sabida murnar wannan auren.


Aure akwai iya adadin matan da aka kayyade wa mutum ya aura zai iya auren daga daya zuwa hudu Amma daganan shikenan aure Sunnah ne Kuma zaman ibada ne sai anyi hakuri Allah kabarmu da masoyanmu.


Zaman aure


Zaman aure wani shafi ne daban da rayuwar Dan Adam domin komai saiya banbanta Dana baya lokacin kana samartaka kokuma rayuwarki zata chanja daga yadda take da a gidan iyayenki angonki kokuma muce mijinki yazama garkuwarki daga wannan lokacin da aka daura muku aure.


Kaikuma namiji kazama magidanci iyali kaima zakayi don haka saika kula sosai Kuma ka kula da tarbiyyar matarka da iyalinka domin sun zama naka zaka fita kanemo sannan Kuma kazo ka Basu domin shine rayuwar auren.


Karanta wannan >> Jarumar kannywood Samira Ahmad tayi abin azo agani


Kekuma ke zaki kula dashi kiyi masa abinda zai faranta masa aduk lokacin da yake bukatarki yazama dole kije matutam kina lafiya babu abinda yake damunki sannan Kuma dole ku sirrinta sirrin junanku idan matsala ce kusan yadda zaku sasanta da junanku basai Kun fita anjiku ba.


Akwai kalubale da yawa kokuma muce jarabawa da ake jarabtarmu bayan aure ko kuga mijin yasamu raunin arziki sakamakon auren dayayi kokuma rikici tsakinin mata da mijin to dukkanin wadannan abubuwan sai anyi hakuri daga baya komai zai zama dai-dai domin za'a Saba.


Nan munyi muku bayani a takaice anan gaba Kuma zamuyj rubutu na musamman data matakin farko har karshe daga lokacin da kakeson yarinya da yadda zakayi har a daura muku aure ki jirayemu zuwa lokaci kadan.
No comments:
Write Comments