Pr ads

Photography

Home YADDA AKE GURASA.


Sannunku dazuwa shafinmu na zazzauloaded sashen girke-girke muna fatan zaku kasance damu a kowacce rana a kowanne lokaci domin samun labarai da fanninka daban-daban na ilmantarwa.


Ayau munzo muku da bayanin yadda akeyin gurasa daga farko zuwa karshe tun daga lokacin da za'a kwaba ta har zuwa lokacin da za'aci ma'ana lokacin da za'a gama gaba dayanta don haka saiku natsu ku karanta dakyau.


Menene gurasa ?.


Gurasa wani nau'in abinci ne da ake gasashi sannan a kwadashi da kuli wasu Kuma sukan sanya masa miya suci ya danganta dai da yanayin yanda suke ci domin ba abinci bane na gida najeria kadai ba.


Karanta wannan >> Yadda ake samosa


Gurasa andade anayinta a duniya musamman a ksashen larabawa suna kiranta da (kubza) saidai tada ta bambanta data yanzu sakamakon da ana amfani da alkama yanzu Kuma akan sarrafa alkamar ne takoma fulawa sai ayi amfani da ita wajen yin abubuwa daban-daban dukkanin abinda alkama zatayi to yawanci fulawa ma zatayi.


Abubuwan da akeyin gurasa Basu da yawa idan kasamo fulawa da yeast shikenan saikuma ruwan sanyi Wanda zaka kwaba dashi, amfanin yeast din shi yake sata ta kumbura wasu sukan sanya ridi a samnata kadan wasu Kuma su barta haka.


Idan kuka samu baho wanda zaku kwaba aciki saiku zuba fulawan ku saka yeast aciki ku juya sosai saiku dauko wanna ruwan sanyin kuzuba aciki Amma saikunyi ahankali saboda kada ku cika ruwa anayinta da danko kamar yadda kike gani a hoto.

Bayannan Kuma sai maganar inda za'a gasa ta wasu suna amfani da kasko mai Fadi irin Wanda ake soya kwai saiku dorasa a wuta yayi zafi saiku dinga yaga Kuna sanyawa a kaskon har ta gasu saiku cire.


Karanta wannan >> Abubuwan da suke kawo mutuwar aure


Wasu Kuma suna amfani da tukunya mai kafa idan kuka Dora a murhu kuka hada wuta sosai sai ku sanya toka a cikin tukunyar kuzuba garwashin wuta a cikin tukunyar kunga dai kenan ciki da waje wuta saiku dinga yaga nanma Kuna likawa ta cikin tukunyar dayayi saiku cire.


Saikuma Wanda suke amfani da asalin tukunyar kasa wacce danan ita anyita ne sabida gasa gurasa Amma yawanci masuyin na sayarwa ne suke amfani da wanna ga irinta Nan a hoto kamar yadda kuke gani a kasa.

Angama kenan da yanda akeyin gurasar da yanda ake gasawa yanzu abu nagaba zamuyi muku bayani akan yadda zaku bandasata da kuli da man gyada kokuma damiya duk dai yanda kukaga damar yinta kowa da yanda yakeso.


Idan kuka dauko gurasar saiku ajiye a gefe saiku debo ruwa a cikin karamin Abu domin wanketa za'ayi idan kuka ajiye saiku dinga dauka Kuma sata Kuna wankewa da sauri sabida karta jike saiku samu faranti mai fadi kusa aciki ku barta.


Karanta wannan >> Waye yafi wani tsakanin nura m inuwa da Umar m sharif


Saiku siyo garin kuli kusanya magi da yaji dakuma gishiri aciki sannan Kuma ku soya man gyada ku tabbatar kunsa albasa aciki sabida yafi kamshi Amma Kuma idan man kuli ne shikena saiku bada kulin akan gurasar kusa Mai shikenan saici idan ma miyane haka.


Saikuma wadanda suke yanka kabeji da kokomba da sauran abubuwa dai irinsu tumatur da albasa duk Karin Dadi ne duk da dai bakowa keso ba Amma Wanda yakeso zai iya sanyawa.


Mungama da wanna darasin saikuma idan munkara haduwa a karo nagaba a wani darasin mungode da kasancewa damu sannan duk abinda baki fahinta ba saikuyi comment domin ayi muku Karin bayani.

No comments:
Write Comments