Pr ads

Photography

Home YADDA AKE SAMOSA.

Barkanku dazuwa shafin zazzauloaded sashen girke-girke ayau munzo muku da sabon Abu kuma mai Dadi mai kayatarwa musamman a wajen hidimar biki, sauka ,walima kokuma taron siyasa da dukkanin wani waje da za'a ci abinci da sauransu.


Shi wannan Abu da muka zo muku dashi yanada sauki wajenyi kuma ko a gidanku zakuyishi batare da bukatan sai kaje wani kichin na musamman ba dukkanin abinda ake bukata a wannan Abu to tabbas za'a sameshi a gida.


Sunan wannan Abu da zamu koyar a yau shine (samosa) wasu mutane dayawa sunsanshi wasu kuma gaskiya suna ji ana yawan fadinsa Amma kuma basusan yanda zasuyi shi ba to yanzu dai zakuji yanda ake yinsa.


Menene samosa ?.


Samosa wani nau'in abinci ne kokuma muce (snacks) da akeyi da fulawa kuma a ci, samosa anayinsa a kasashen duniya daban-daban musamman kasar India birin Delhi suna yawan amafani dashi idan kaje gidajen cin abincinsu a wararen.


Abubuwan da akeyin samosa.


Kafin ka fara aikin samosa yakamata saika nemo dukkanin abubuwan da ake hadawa sannan kafara aikinka saboda gudun matsala karka fara Kuma kazo baka samu want abunba.


1. Fulawa.
2. Kwai.
3. Nama.
4 Maggi.
5. Kori.
6. Gishiri.
7. Mangyada.
8. Attarugu.
9. Albasa.
10. Karas.
11. Ruwa.
12. Baking powder.Wadannan abubuwan da muka lissafa guda goma sha biyu dai-dai sune akeyin samosa dasu, matukar kana bukatar samosanka yayi Dadi sosai to tabbas saika nemo wadannan abubjabu dana lissafa kafin kafara aikin ka.


Yadda ake hadawa.


Idan ka dauki fulawa kazuba a robanda zaka kwaba saika dauko kwai kafasa kazuba a ciki kasanya baking powader da gishiri kadan a ciki wasu sukan sanya magi a ciki Amma idan kanaso saika saka kadan idan kuma bakaso shikenan.


Tunda kasa gishiri dama amfaninsa saboda kar aji wannan fulawan salam-salam babu dandano ko kadan shiyasa muka zabi kasanya gishiri da magi Koda kadan-kadan ne.


Saika dauko ruwa kazuba ka kwabashi da karfi yafi na cin-cin ruwa yanda dai kasan idan ansashi a injin murza taliya zaiyi batare da wata matsala ba domin kunga idan yayi ruwa to bazaiyiwu ya niku a injin ba.


Bayan Kun kwaba shi zaikiu ajeshi a gefe ki dauko wannan naman ku wanke ku tafasa shi da magi da kori da gishiri idan ya tafasa saiku saukeshi ku jajjaga attarugu ku yanka albasa da magi ku zuba a cikin namannnan sauku nika shi ku aje a gefe.Wannan karas din shikuma saiku wanke ko samu abin goga karas ku gogashi kanana sosai saiku hada a cikin wannan naman ku juyashi sosai, wasu sunayi ko babu karas din Amma idan baku samuba zaku iyayinshi haka.


Bayan Kun gama saiku sa Mai kadan a kaskonku kuzuba wannan naman ku soyashi sama-sama karya soyu sosai saboda kunsan bayan an nadashi da wannan fulawan sai ankara soyawa.


Saiku dauko wannan fulawan da kuka kwaba saiku nikashi a injin taliya ku yankashi saiku dinga zuba naman aciki ki nade shi kamar yanda kuke gane a hoton da yake kasa.


Da zarar Kun gama duka sauku Dora man gyadanku a wuta idan yadau zafi saiku sa albasa saboda man gyadan yayi kamshi saiku dinga soya Wannan Wanda kuka nada.


Anan mukazo muku karshen wanna bayanin akan yadda ake samosa sai aje ayiwa ango domin yaci yaci Dadi, kamar dai kullum muna fada muku kuci gaba da kasancewa da wannan shafin namu dakuma sauran kafafen sadarwa mungode.
No comments:
Write Comments