Pr ads

Photography

Home ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA.
Barkanku da shigowa wanna shafin namu musamman wannan Shirin da zamu baku samfurin kalaman soyayya a wannan zauren namu na zauren masoya, saiku tsaya dakyau wannan wanna dai na maza ne Amma kuma mata zasu iya amfani dashi saisu juyashi misali inda akace kinzamo saiki rubuta kazamo fatan zaku ji dadin wannan kalamai.


1. Inama ace nazamo a tare dake a dukkanin bugun numfashi na kaunarki kullum tana Kara girma a cikin zuciya ta dake nake kwana masoyiyata a zuciyana haka kuma dake nake tashi bayyanar murmushinki a fuskarki Yana karamin shauki a kids yaushe.

2. Masoyiyata kisani Allah ya azurta rayuwarki da abinda mata dayawa suke da burin samu Amma Basu samuba kisani ke ta daban ce a cikin zuciya ta Kuma haka nima ina fatan na zamo na musamman a cikin zuciyarki abar kaunata.

3. Rabin rayuwata kisani hakika mata irinku kadan ne domin da za'a kawo mini littafi da abin rubutu na rubuta irin baiwar da Allah yayi Miki da nayi littafai dayawa cike da tarin kalmomi ke ta musamman ce a wurina.

4. Idan kika daga kanki da daddare zakiga sararin samaniya cike da taurari shikuma teku cike da ruwa doron kasa Kuma cike da ciyayi Amma Ni cikin zuciyata cike take da soyayyarki babu kuma sauran wurin da za'asa want Abu.


Karanta wannan >> Bayani akan zaman aure


5. Kafin na kwanta bacci ina kwantawa da tunaninki haka Kuma idan ina barci nakanyi mafarkinki dazarar na farka saina kalli hotonki sannan nake jin Dadi na dawo cikin hankalina.

6. Soyayyarmu ni dake ba Mai karewa bace domin ko Bayan babu Raina kema babu ranki to hakika ruhina da naki suna atare har lokacin da zamu hade a aljanna a matsayin mata da miji.

7. Ki tausaya wa zuciyar datayi nisan a kaunarki harta kusa nakasa kada zugar mahassada tasa ki juya mata baya domin hakan shin zai haifar min da raunin da bazai taba warkewa ba azuciyata.

8. Tsananin kaunarki ya dankare a cikin zuciyata kamar yadda kwakwalwar dan'adam take a dankare a kansa ki tallafa ma zuciya ta kada ki sanya tayi hawaye da zata iya fitowa Dana fito Miki da ita domin ki Kara gasgata zancena.

9. Amincin Allah ya Kara tabbata a gareki yake wacce tafi tauraro da dukwani haske a idanuwana ina fatan kina lafiya kamar yanda nake a koda yaushe ina yawan tunaninki domin babu wani Abu da zaisa na Manta dake ba.

10. Hakika daga jiya zuwa yau wani bakon bakinciki ya bakunci zuciyata dalili kuwa shine rashin Jin munyarki da banyiba duk inda kike Ina fatan dai kina lafiya.

11. Me kaunata kece farincikin Raina Kuma kece kofar zuciyata dukkanin Wanda zai shiga ke zai taarar idan kikaga want to tabbas ke kika bayar da hanyar inajin Dadin kasancewa dake a koda yaushe.


Karanta wannan >> Abubuwan da suke kawo mutuwar aure


12. Dake nakeson na Kare rayuwata dake nakeso na zauna har karshen rayuwata ina alfahari dake Rabin Raina a koda yaushe mukwana lafiya kiyi barci me Dadi.

13. Nagode da Irin kulawar da kike nunamin a kullum zamanmu a tare shine farincikina rashinki shi zai sanyani cikin halin bakinciki da damuwa ina fatan zakici gaba da bani kulawa.

14. Nazari na da tunanina a kullum Bai wuce akan yadda zakayi naga munyi aure ba ki Kira hakuri nasa kinyi Allah zai kawo mafita watarana zaki ganni a matsayin angonki kekuma amarya.

15. Daga lokacin Dana fara ganinki tunani na da komai ya tsaya babu abinda nake kallo a idona saike Koda rufe ido kuwa nayi hankalina Bai dawo jikina ba Saida na furta Miki ina sonki.

16. Yau da gobe akwana a tashi inata yankamiki filayen da suke cikin zuciya ta da alamu nanda wani lokaci zai zamto gabadaya ke kike da mallakin zuciya ta me kaunata nikuma zanyi farinciki da hakan.

17. Ina kuka a duk lokacin dana tuna da wata rana wacce zaki kirani Amma bazan amsaba ranar da numfashina ya Kare a duniya itace ranar rabuwa tun yanzu inajin wannan radadin a zuciya ta.

18. Ina Mai baki hakuri gimbiya ta kinkirani bana kusa kinmin massage bakiga reply ba hakan yabiyo bayane sakamakon rashin chaji a wayana nakai chaji kiyi hakuri ban fada Miki tun Farkon ba ina fatan zaki amshi uziri na.


Karanta wannan >> Waye yafi wani tsakanin nura m inuwa da Umar m Sharif.


19. Ni da kaina bansan irin soyayyar da nake Miki ba Kuma bansan adadinta ba idan Kuma kinaso kisan Irin soyayyar da nake Miki ki daga Kai da daddare ki irga yawan adadin taurarin da suke sama inda kin iya to soyyarki tanada adadi idan Kuma baki iya ba to soyayyarki batada adadi a zuciyata.

20. Nayi Miki alkawarin matukar ina raye bazaki taba kuka ba ni Zan share Miki hawaye bazan barki Kisha wahala ba Zan kula dake Kuma na rike alkawarin soyayyarmu.


Wannan munkawo Muku zafafan kalaman soyayya guda ashirin sannan muna Nan zamuci gaba ahakali zamuyitayi domin mu bayar da gudun mawarmu ga masoya.

Yakai Mai karantawa munaso kayi comment da Wanda yafi burgeka daga 1-20 hakanne zai Kara Mana kwarin gwiwa akan abinda muke mungode.


No comments:
Write Comments