Advertise On Nairanet

Header Ads

BABU TABBAS MU SAYI SABABBIN YAN WASA A WANNAN KAKAR INJI P.PEREZ.

Babu tabbacin mu saya sababbin yan Wasa a bana inji florentina Perez shugaban kungiyar kwallon kafa ta real madrid duba da yadda muka kashe makudan kudade a kakar wasan data gabata Kuma yanzu kungiyar tashiga wani yanayi na rashin kudi.


Bayan tashi daga wasan laliga na karshe da real Madrid tasamu nasarar cinye kofin laliga na bana 2019-2020 shugaban kungiyar yayi bayani duba da yadda sukayi siyayya a Farkon wannan kakar wasan data gabata.


Real Madrid sun sayi manyan yanwasan gaba domin matsalar da suke fama da ita na rashin masu zura kwallo a raga  inda duk da haka kungiyar take matukar bukatar gyara sun sayi yan Wasan gaba guda uku.


Hazard sun dauki daga kungiyar kwallon kafa ta Chelsea akan yuro miliyan dari (£100m) sedai rauni ya hanashi yai abin kirki inda ya bayyana wannan kakar a matsayin kakar Wasa mafi muni a gareshi.


Luka jovic Dan asalin kasar Serbia Wanda yake taka leda a Frankfurt a gasar kasar Germany Shima sun sayeshi a kan kudi yuro miliyan sittin (£60) shikuma haryanzu baisamu cikakkiyar dama ba da zai nuna kansa a kungiyar har suke tunanin turshi zaman aro kokuma akasin hakan.


Rodrygo Silva matashin Dan wasan Santos Dan asalin kasar Brazil Mai matukar hatsari a gaban raga ya kasance yaro Dan shekara goma Sha takwas zuwa sha Tara (18-19) Amma Kuma ya nuna kansa a filin wasan cikin nasarar daya samu harda kwallo uku rigis daya jefa a gasar cin kofin nahiyar zakarun turai a ragar galatasaray, Wanda tasaya akan kudi yuro miliyan arbain da biyar (£45).


Sedai dukda wannan siyayyar da kungiyar tayi zata saurara ta kara dubawa a kakar Wasa me zuwa inda suke zawarcin manyan yanwasa da suka hada da mbappe,neymar dakuma Sterling Amma Kuma babu tabbacin daukar yan'wasan a bana.


Haka kuma kungiyar tashirya rabuwa da yan wasanta guda uku zuwa hudu sannan Kuma zata tura wasu zaman aro acikin yanwasan data bayyana zata sayar nafarko shine Gareth bale duba da yadda Dan wasan ya Daina kokari a filin wasa Kuma da yananin rashin jituwa tsakaninsa da mai horas da kungiyar zidane.


James rodrigues shine nabiyu Shima akwai rashin jituwa sosai a tsakaninsa da zinade zidane inda baya samun damar buga wasanni tun bayan dawowarsa zaman aro daga kungiyar Bayern Munich ta kasar geemany.


Mariano Diaz shikuma Yana yawan samun rauni hakan yasa kungiyar ta fara tunanin rabuwa da Dan wasan sedai shikuma Yana son Zama a kungiyar Dan wasan Dan dominant republic.


Sedai Kuma komai zai iya faru akan sauran yan wasan irinsu Luka modric, brahim Diaz inda suke tunanin sayar da modric indai Martin ødegaard  zai dawo daga zaman aron da yakeyi a kungiyar kwallon kafa ta real sociedad a bana.


KALAMAN ZIDANE BAYAN YASAMU NASARAR LASHE GASAR LALIGA 2019-2020.


Mai horas da yan wasan real madrid ya bayyana cewa tabbas munyi kokari munyi nasara munsamu dama Kuma munyi amfani da damarmu Wasa yayi kyau Kuma hakan muke bukata kowa da kowa cikin yan'wasan mu yayi kokari don ganin mukai ga nasara.


Amma Kuma duk da haka akwai aiki a gabanmu sosai domin yanzu zamu maida hankalinmu ne akan wasanmu da gaba na kofin nahiyar zakarun turai da zamu ziyarci gidan Manchester city a filin Wasa na ettihad.


Muna bukatar muga munyi nasara domin tsallakawa Wasa na gaba domin muna bukatar mu kashe wannan gasar a karo na 14.

Post a Comment

0 Comments