Pr ads

Photography

Home HANYOYIN SAMUN KUDI || ZAZZAULOADED.COM.NGBarkanku da zuwa wannan shafin namu Wanda muka saba kawo muku abubuwan daban-daban ayau hanyar da mukazo muku da ita hanyoyi ne da zaka samu kudi dasu idan kabin abin yadda yake tareda bayarda shawar-wari.


Idan mukace hanyoyin samun kudi bawai muna magana akan Abu daya kacan bane aa muna magana ne akan abubuwa dayawa ma'ana haryar ba guda daya bace kacal.


Zamu fara da bangaren sana'a tareda yimuku bayani akai dakuma yadda zakayi domin ganin mun hadu mun kawar da rashin aikinyi kokuma domin kawar da talauci a wannan lokacin musamman yanda abubuwan suka chanja.


Akwai sana'oi daban-daban Wanda mace zatayi namiji Shima zaiyi dukda cewa wasu lokutan muna raina sana'ar ne muna ganin munfi karfinta kuma Sam bahaka bane dukkanin hanyar da akace za'a samu kudi to baikamata ace anyi Wasa da ita ba.


Karanta wannan >> Yadda ake gurasa.


Musamman ga yara samari kabar gani kana makaranta idan yazamto bakada sana'a Babu Mai tallafa maka tayaya karatun zai yiwu, haka Suma yan'mata akwai sana'oin da suna zaune a gida kokuma a kofar gida zasuyi Kuma su Sami abinda sukeso ko Babu yawa.


DAGA CIKIN SANA'OIN DA MATA ZASU IYAYI.


1. Alawar madara.
2. Gurasa.
3. Cin-cin.
4. Zobo.
5. Kunun aya.
6. Donot.
7. Awara.
8. Fanke.
9. Koko ko kunu.
10. Gyada.


Wadannan dana lissafa guda goma duka kananun sana'oi ne Wanda mace zata iya dogara dasu matukar zata tsaya ta gyara bama iya mace ba har maza akwai Wanda zasu iyayi kamar cin-cin, donot, dakuma gurasa.


Sannan akwai saye da sayarwa kamar kasiyo Abu naira goma kasayar naira goma Sha biyar akwai kayan su Maggi dasu omo duk wannan abun hanyoyine da mutum zai samu kudi Amma Wai kaga mutum yarasa sana'a sedai bashi da niyyar yin sana'a.


SANA'OIN DA MAZA ZASU IYAYI.


To shudai namiji ba kamar mace bane zai iya fita ko'ina domin yaga yasamu abinda zai rufa ma kansa asiri ba lallai sai sana'ar wuri daya ba zaka iya talla ka dinga zagawa ba lallai sai area dinku ba sai katafi wani wurin daban idan bazaka iyayi a unguwarku ba daika nemi sana'a kamar ;


1. Wankin mota.
2. Wankin Kaya.
3. Gyaran takalmi.
5. Kodago.
6. Aikin gini.
7. Sana'ar shayi.
8. Yankan farce.
9. Guga.
10. Aikin fawa.


Wannan Dana lissafo kusan kowa zai iyayi indai namiji ne Kuma yawanci basaida jari ba mutum zaifara Wanda yake bukatar jari shine kamar shayi haka wannan Saida jari Amma akwai dabarorin sana'a da zamu kawo duk zaku fahinta komai cikin sauki.


Karanta wannan >> Zafafan kalaman soyayya.


Amma kafin naje ga wannan zanyi wani bayani yakamata yara suna kanana a kaisu waje koyar aiki ta yadda yaro zai taso da sana'arsa a hannu ba tareda ya wahala ba akwai wajen sana'oi da dama kamar koyan dinki, walda, kanikanci gyaran mashin da mota.


DABARORIN SANA'A.


Idan ya kasance bakada kudi Kuma kanason yin sana'a to meyakata kayi ? Kanemo duk abinda kake buka misaki zakayi alawar madara daga cikin abubuwan da ake hadawa akwai madara, sugar sai itacen da zaka dafa sugar din da flavor.


Saikaje wurin me madara kuyi magana yabaka madara idan kayi kasayar zaka bashi kudin sai ka dauki wata sabuwa haka me sugar dama dai duk abunda kake da bukata kafin fara wannan sana'a idan yabaka kaga bakada damuwa saika fara sana'arka.


Kanayi tun ahaka ribar da kake samu idan katara shikenan sai jarin yazama naka kaga kayj dabara tun baka da kudi har kasamu naka sai kaci gaba da juyawa kudin harma idan kanason gwada wata sana'ar saikayi.


Karanta wannan >> Bayani akan zaman aure.


Akwai Kuma sana'ar kamfani kamar inda sukeyin pure water ko bread kodai wani abun Suma zaka iya zuwa kasamu manager na kamfanin kuyi magana akan idan kadauki Kaya kasayar zaka dawo da kudin abaka wani kayan.
No comments:
Write Comments