Pr ads

Photography

Home SABON TSARIN MTN NIGHT BROWSING.Sabon tsarin mtn night browsing tsarine a baya da ake siyan data me sauki ake amfani da ita tsawon wasu awanni kamar yanda muka sani bawai data bane da takeyin amfani har wasu kwananki kokuma watanni.


Zamuyi bayani yadda abun yake domin wadanda basusaniba Suma zasu iya amfani da wannan damar suma suci gajiyar wannan datar domin tanada sauki sosai Kuma tanada yawa.


Wannan datar tabbas dukda Bata da tsawon awanni amma Kuma zatayi maka dukkan wani irin Abu da zakayi a yanar gizo Kuma wadanda zasuci fin moriyar wannan to masu downloading na video,waka,app da sauran abubuwa.


Kuma bawai anwareta bane ance iya Abu daya zakayi ba kunsan akwai datar da takeyin Facebook zallah akwai wacce take whatsapp itama sannan akwai datar Instagram to it' wannan ba'a ware ance ga ta Abu daya ba zakayi dukkan abinda akeyi a yanar gizo (internet).

Karanta wannan >> Farashin datar mtn a 2020.

Datar tana daukar tsawon awa  bakwai (7hrs) zuwa awa takwas (8hrs) ana amfani da ita Saida Kuma a wannan kwanakin ne kamfanin mtn ya chanja tsarin ba kamar yadda muka sani a baya ba Don haka yanzu zanyi bayanin bambamcin da aka samu tsakani.


Duk wani Wanda yake night browsing yasan cewa ana farawa ne misalin karfe shabiyu na zuwa karfe biyar na asuba inda yanzu Kuma tsarin ya chanja zaka iya siya misalin shadayan dare Kuma kayi amfani da ita a maimakon shabiyun.


Amma Kuma zaka iya siyan datar kafin lokacin amfaninta ya fara kamar karfe gima misali kasiya saikuma karfe shadaya kafara amfani da datarka babu wani matsala a maimakon sai lokacin yayi da zaka fara ka tsaya ka siya.


Abaya zaka iya siyan 500mb ne kacan inda yanzu Kuma suka kara zaka iya siyan datar takai 1gb kunga ansamu kari kenan akan yadda ake siya a baya zaka iya siyan 250mb har sau biyu kokuma 500mb sau daya yanzu kuma 500mb sau biyu kokuma 250mb sau hudu.


Ga wadanda sababbi ne a harkar wannan datar sukeso Susan yadda akeyi to yanzu zanyi bayaninta yadda zakayi daga farko har zuwa karshe Amma dai ka tabbatar layinka mtn pulse ne domin shine layi daya tilo da yakeyi.

Karanta wannan >>Bayani akan zaman aure.

Idan Kuma ba a tsarin MTN pulse kake ba to zaka iya mayar da layinka yakoma MTN pulse din cikin minti biyar ba sai an Dade ba Amma dai kawai ka tabbatar akwai katin naira dari a layin domin idan bahaka ba bazaiyi ba.


YADDA AKE KOMAWA MTN PULSE.


Ka saka katin naira dari a layin idan Kuma akwai aciki shikenan sai ka danna *496*1# shikenan sai kayi migrating zasuyi maka massage kana fita kaduba zakaga tsarin naka ya chanja zuwa MTN pulse din da kake bukata.


FARASHIN DATAR.


Duk 250mb ana sayarwa kan naira ashirin da biyar (N25) kokuma kasiya 500mb naira hamsin (N50) kunga kuwa ai wannan datar tayi sauki sosai za'a ci moriyarta kwarai da gaske domin bana tunanin akwai wacce takai wannan sauki.


YADDA AKE SAYAN DATAR MTN NIGHT BROWSING.


Bayan kasa kudi a layinka kukuma daman akwai kudi na iya adadin datar da kakeso Amma yazama kudin sunkai saika dannan *406*3# shikenan saika zaba ta nawa kakeso kasiya idan takare zaka iya kara siya domin kaci gaba da aiki da ita.
No comments:
Write Comments