Pr ads

Photography

Home YADDA AKE SARRAFA FULAWA.


Yadda ake sarrafa fulawa acikin sauki kamar yadda muka sani fulawa ana iya sarrafa ta abubuwa da yawan gaske Wanda yanzu yakasance kusan  zamu iya cewa kaso saba'in da cikin abincin da mukeci duk fulawa ne musamman a arewacin kasarmu ta nigeria.


Sabida haka mukaga yadace mu kawo muku hanyoyi kala-kala na yadda zaku sarrafa taku fulawar wata kila kunayin wani Abu daban Kuma ya isheku Kuna bukatar ku sauya want kunga wannan zai matukar taimaka muku.


Abunda yake yanzu ya kamata muyi zamu lissafo muku abubuwan da akeyi da fulawa cikin sauki dukda dai wasu anayinsu da oven abin gasawa wasu Kuma akan soyasu a Mai Amma sai zaku duba kuga Wanda zaku iyayi sannan bayn mun lissafu zamuyi cikakken bayani akan guda daya Wanda daga baya zamuci gaba.


ABUBUWAN DA AKEYI DA FULAWA.


1. Concot.
2. Cin-cin.
3. Gurasa.
4. Donot.
5. Taliya.
6. Dubulan.
7. Bredi.
8. Cake.
9. Meat/fish pie.
10. Fanke.
11. Biskit.
12. Dan-wake.
13. Wainar fulawa.
14. Alkubus.
15. Funkasau.


Karanta wannan >> Hanyoyin samun kudi.


Ga kadan nan na lissafo daga cikin abubuwan da akeyi da fulawa dukda nasan ko rabi ban fado bah amma nasan wadannan ma zaku karu dasu sosai idan Allah ya yarda Kuma zamu dauki daya aciki muyishi ta yadda kowa zai fahimta.


Zamu dauki na farko wato (concot) Wanda gaskiya kamar zai Zama bako sabo daga cikin abubuwan Dana lissafo shiyasa na dauko Shi domin nayi Mana bayaninsa Kuma bawai you agida kawai ba zaku iyayi domin sana'a ce sosai Kuma yanada matukar riba Mai yawa.


YADDA AKE CONCOT.


Abubuwan da zaka nema kafin ka kwaba Shi saika tabbatar suna gefenka sabida gudun kar afara azo arasa wani abun kunga shiri ba baci kenan sedai ayi wani abun ko afasayi gaba daya.


1. Fulawa.
2. Sugar.
4. Yeast.
5. Baking powder.
6. Gishiri.
7. Manja.
8. Man gyada.


Wadannan sune jerin abubuwan da zamuyi amfani dasu wajen Yin wannan concot din saiku natsu ku karanta dakyau sabida gudun kuskure kar azo ayi baiyiba ko baiyi dadi ba kunga Rai bazaiso hanaka ba Don haka zamu fara.


Karanta wannan >> Hausa Novels littafin kanwar mister.


Asamu baho Wanda za'a kwaba aciki sai a zuba fulawan asaka sugar da baking powder sai asaka gishi kadan da manja sabida yayi ja yafi bayar da kala kowa yagani zaiyi sha'awarsa.


Sai asamu ruwan zafi Amma fa ba zafi sosaiba dumi dai kawai kada yazama yayi sanyi dai sai akwaba dashi sannan kuma kwabin yayi tauri bawai ruwaba sai adauka akai gidan biredi aci su nikashi a injin Nika biredi saiku biyasu baya wuce naira hamsin zuwa dari.


Dagana ana kawo Shi zakuga yayi laushi sosai saiku samu faranti na silver ku yanko kadan kusa saikusa kwalabar coke ko tawani Abu kuyi Fadi dashi ku yankashi kamar yanda kuka gani a wannan hoton da yake kasa.


Shikenan saiku yankashi duka kusa a keda Mai Fadi idan baiyi tashi ba saiku samu wani ledan Shima me Fadi ku rufeshi zakuga ya tashi ya kumbura shikenan saiku Dora Mai a wuta yayi zafi saikusa albasa ku soyashi yayi kamshi sai ku dinga dauka Kuna siyawa a cikin man gyadan.


Idan nagida ne Wanda zakuci duk yanayin girman da kukayi Babu damuwa Amma idan na sayarwa ne zaku tsaya dakyau ku daidaita girmansa sabida yanayin abubuwan anayin sana'a Don riba ne idan yayi girma dayawa kunga baza'a fitaba.


Karanta wannan >> Yadda ake gurasa me dadi.


Bayani Wanda kuka zuba a cikin man gyada yasoyu zaku ganshi yayi jyau yayi Shar tayadda ko fita akayi dashi za'a sayar dashi da sauri Shima ga yanayin yadda yakeyi a wannan hoton Shima da yake kasa.


Nan muka kawon karshen wannan Shirin na filin girke-girke saikuma idan munhadu a gaba
Mungode.No comments:
Write Comments