Pr ads

Photography

Home HANYOYIN KARA KIBA.Barka dazuwa wannan shafin namu wanda a yau zamuyi bayani akan abubuwanda suke saka mutum kiba akwaisu dayawa Amma zamu kawo muku misali dakuma Wanda yadace ayi amfani dashi.


Akwai abubuwa da dama da suke sanya mutum kiba Wanda Kuma wasu daga ciki suna cutarwa dukda zamu kawosu saboda kusansu Amma kuma zaifi kyau kuyi amfani da Wanda muka baku a shawara akai tunda angwada anga Yana aiki yanda yakama.


1. Yawan Shan zaki : Yana sanya mutum kiba kiba dukda munsani cewa zaki Yana iya haifar da wasu cututtuka a jikin Dan adam Amma bazamu dauki wannan a matsayin abinda zamuyi amfani dashi wurin kara kiba ba.


Karanta wannan >> Yadda ake sarrafa fulawa.


2. Yawan cin maiko : Shima yawan cin maiko Yana  sanya mutum kiba Kuma munsan maiko abune da muke amfani dashi yau da kullum. 


3. Rashin  motsa jiki : kowa yasan komai kibarka indai kana motsa jiki yanda ya kamata to sai kibarka ta ragu musamman idan kana gudu, kwallo, da sauran wasu aikace-aikace da gida da zasu zamto ana motsa jiki ne.


4. Cin  naman saniya : Naman saniya Yana matukar taimakawa wajen kara kiba dukda shima akwai  shekarun da idan kakai zai zamo maka illa kamar yadda masana suka fada Yana iya zamawa mutum a cinya kamata yayi kamar daga shekara 50 ko kasa da hakama ka kaucewa cin naman saniya saika kima kifi ko naman zabo, dawisu, kajin hausa da Naman tantabara zaifi kyau ga lafiyarka.


Karanta wannan >> Yadda ake gurasa.


5. Yawan cin protein : Cin protein kamar kwai a wasu lokutan muna daukan cin kwai a matsayin jindadi ne muci dayawa aa ka'ida shine kaci daya a Rana shine zaiyima amfani Kuma zai taimaka maka wajen kara kiba.


HANYAR DAYA DACE KUBI DOMIN KARA KIBA.


Wannan hanyar da zamuyi bayani yanzu itace da dace mutum yabi wurin kara kiba domin ba kwaya bace ta bature kokuma wani sassaken itace aa kunu ne akeyi asha batare da wani damuwa ba.


ABUBUWAN DA ZA'A SAMU.


1. Waken soya cokali biyu.

2.Ridi cokali biyu.

3. Dabino guda biyar.

4. Hulba cokali daya.

5. Gyada dai dai misali. 

6. Madarar gari cokali biyar.


Karanta wannan >> Zafafan kalaman soyayya.

 

yadda zaku hada ku soya waken soyan harsai yafara kamshi sai sauke a nika kokuma daka ya zamto gari shima ridin haka zaku masa ku soya shi ku mayar dashi gari  shima wannan dabinon ku daka yakoma gari ku hada da hulbar da madarar itakuma gyadar sai a hada kunun gyada da ita saiku dinga diban wancan abubuwan da kuka hada kunayin kunun harna tsawon sati biyu zakuyi mamaki.

No comments:
Write Comments